Tashin nakiya a coci: Ana ta zaben fidda gwani, Tinubu ya tafi jihar Ondo ziyara

Tashin nakiya a coci: Ana ta zaben fidda gwani, Tinubu ya tafi jihar Ondo ziyara

  • A halin yanzu dai Bola Ahmed Tinubu yana can jihar Ondo biyo bayan mutuwar wasu masu ibada a coci a hannun wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne
  • Tinubu yana tare da Gwamna Rotimi Akeredolu wanda ya fito daga yankin da lamarin ya faru a yayin ziyarar
  • Sama da mutane 50 ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani abin da aka kwatanta da kisan kiyashi inda aka harbe maza da mata da kananan yara

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ondo - Tsohon gwamnan jihar Legas kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya dura jihar Ondo domin jajantawa iyalan wadanda aka kashe a wani babban cocin Katolika na St Francis da ke Owo a ranar Lahadi, 5 ga watan Yuni.

Kamar yadda wani dan takaitaccen hoton bidiyo da Legit.ng ta samu a shafinsa na Tuwita, Gwamna Rotimi Akeredolu yana tare da Tinubu a cikin wata mota inda suka nufi karamar hukumar Owo domin ziyartar wadanda abin ya shafa.

Kara karanta wannan

2023: Kowa ya cije kan bakansa, an gaza yin sulhu da Tinubu da su Osinbajo a takaran APC

Kalli bidiyon:

Tinubu ya kai wannan ziyara ne daidai lokacin da jam'iyyar APC ke ci gaba da kokarin shirye-shiryen yin zaben fidda gwani na shugaban kasa da ke gudana a Abuja.

Allah wadai

Tun da farko, Tinubu ya fitar da sakon ta’aziyya ga wadanda abin ya shafa da kuma al’ummar Ondo ta wata sanarwa da ya yi sa’o’i shida kafin isowarsa jihar Ondo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Legit.ng ta rahoto a baya, Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin takaici, inda ya ce babu inda mai hankali zai yi irin wannan barna da kashe rayukan da ba su ji ba ba su gani ba.

Jigon na jam’iyyar APC ya kuma yi kira da a damke masu aikata miyagun laifuka domin a yi musu cikakken shari’a da yiwa wadanda lamarin ya shafa adalci.

Kaduna: Gobara ta tashi a kwalejin ilimi ta Zaria, ta barnata kwamfutoci 100

Kara karanta wannan

Buhari ya yi Allah wadai da harin cocin Ondo wanda ya kai ga kisan masu ibada

A wani labarin, sama da kwamfutoci 100 ne suka lalace a wata gobara da ta tashi a Sashen Kwamfuta na Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Zaria a Jihar Kaduna, rahoton Daily Trust.

Jami’an kashe gobara sun dauki tsawon lokaci suna gwabzawa domin shawo kan gobarar da ta tashi da misalin karfe 9 na safiyar ranar Asabar lokacin da ma’aikata ba sa wurin aiki.

Shugaban kwalejin, Dakta Suleiman Balarabe, ya ce gobarar ta tashi ne daga wata na'urar hana katsewar wutar lantarki (UPS).

Asali: Legit.ng

Online view pixel