Rikici ya ɓarke a Sakatariyar APC ta Abuja bayan ɗan takarar shugaban kasa ya jefa kyautar N50,000

Rikici ya ɓarke a Sakatariyar APC ta Abuja bayan ɗan takarar shugaban kasa ya jefa kyautar N50,000

  • Danbarwa ta barke tsakanin direbobi, jami'an tsaro da masoyan APC bayan gwamna Umahi ya watsa kyautar N50,000 a Abuja
  • Bayanai sun bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasan ya watsa kudin ne yayin da yake gab da shiga Mota a Sakatariyar APC ta ƙasa
  • Gwamna Umahi ya ziyarci babbar Sakatariyar ne domin ganin shugaban jam'iyya, Sanata Abdullahi Adamu

Abuja - Direbobi, jami'an tsaro da masoyan jam'iyyar APC sun ba hammata iska kan kyautar tsabar kudi da gwamna Ebonyi, Dave Umahi, ya wurga musu, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Gwamna Umahi ya ziyarci babbar Sakatariyar APC ta ƙasa ne domin gana wa da shugaban jam'iyya, Sanata Abdullahi Adamu, kwanaki biyu bayan kwamitin da John Oyegun ke jagoranta ya tantance shi a Abuja.

Gwamna Dave Umahi.
Rikici ya ɓarke a Sakatariyar APC ta Abuja bayan ɗan takarar shugaban kasa ya jefa kyautar N50,000 Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Bayan ganawarsu wacce ta gudana cikin sirri kuma ta shafe sama da awa ɗaya, Gwamna Umahi ya amsa tambayoyin manema labarai daga nan ya nufi motarsa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya saki sabon Bidiyo, ya faɗi inda zai nufa idan ya sha ƙasa a zaɓen fidda gwanin APC

Yayin da ya je gab da shiga cikin motar, Umahi ya juyo sannan ya jefa ɗaurin tsabar kudi N50,000 ga dandazom mutanen da ke wurin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakan da gwamnan ya yi ya ta da yamutsi yayin da magoya bayan APC, Direbobi da jami'an tsaro suka bai wa hammata iska a kokarin samun rabon su daga kudin.

Umahi na ɗaya daga cikin yan takarar shugaban ƙasa karkashin APC guda 23 waɗan da suka kai kansu Otal ɗin Transcorp Hilton a birnin Abuja.

Sauran yan takarar APC da aka tantance

Sauran yan takara 22 sun haɗa da, Bola Tinubu, Rotimi Amaechi, Fasto Tunde Bakare, Chukwuemeka Nwajiuba, Gwamna Muhammed Badaru, Sanata Ajayi Borroffice, Sanata Ibikunle Amosun, Ken Nnamani, da Fasto Nicholas Felix.

Sai kuma Yemi Osinbajo, Ahmad Lawan, Godswill Akpabio, Dimeji Bankole, gwamna Yahaya Bello, gwamna Ben Ayade, gwamna Kayode Fayemi, Ogbonnaya Onu, Ikeobasi Mokelu da Sanata Rochas Okorocha.

Kara karanta wannan

Gwamna ya faɗi wanda APC zata tsayar shugaban kasa idan har tana son cigaba da mulki a 2023

A wani labarin kuma Gwamna Badaru na Jigawa ya ce yana kyautata tsammanin shi zai lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023

Gwamna Muhammed Badaru Abubakar na Jigawa ya ce fatansa na lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na APC ya girma sosai.

Gwamnan, wanda ke fatan gaje shugaba Buhari a 2023, ya ce ba tare da baiwa Deleget kuɗi ba zasu zaɓe shi saboda wasu dalilai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel