Bayan canza zaɓe, Ɗan tsohon gwamna ya lallasa tsohon shugaban FCC, ya lashe tikitin takarar gwamna a 2023

Bayan canza zaɓe, Ɗan tsohon gwamna ya lallasa tsohon shugaban FCC, ya lashe tikitin takarar gwamna a 2023

  • Ɗan tsohon gwamnan Kwara da Allah ya yi wa rasuwa, Hakeem Lawal, ya lashe zaɓen fidda gwanin SDP na takarar gwamna
  • A zaɓen wanda aka canza, Hakeem ya samu kuri'u 606, ya lallasa tsohon shugaban FCC ta ƙasa, Mista Oba, mai kuri'u 177
  • Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta sake shirya zaɓen ne bayan korafin da Oba ya shigar mata kan na farko

Kwara - Ɗan marigayi tsohon gwamnan jihar Kwara, Hekeem Lawal, ya lashe tikitin takarar gwamnan Kwara na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaɓen 2023.

Daily Trust ta rahoto cewa ya lallasa tsohon shugaban hukumar gyaran hali (FCC) ta ƙasa, Farfesa Shuaib Abdulraheem Oba, a zaɓen fidda gwani da aka canza a Ilorin.

Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).
Bayan canza zaɓe, Ɗan tsohon gwamna ya lallasa tsohon shugaban FCC, ya lashe tikitin takarar gwamna a 2023 Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Hakeem ya samu kuri'u 606 wanda ya bashi damar lallasa Mista Oba, abokin hamayyarsa ɗaya tilo, wanda ya samu kuri'u 177. Kuri'a guda Takwas kuma ta lalace.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya faɗa mana ɗan takarar da yake son ya gaje shi a 2023, Gwamnan arewa ya fasa kwai

Zaɓen fitar da ɗan takaran wanda ya samu halartar jami'an hukumar INEC masu sa ido, ya na da Deleget 772, huɗu daga kowace gunduma 193 na Kwara tare da wasu shugabannin jam'iyya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Meyafaru a zaɓen farko da ya gabata?

Ɗan tsohon gwamnan kuma ɗan takara a SDP ya lallasa abokan takararsa a zaɓen fidda gwanin farko da ya gudana ranar Laraba ta hanyar amfani da Deleget kaɗai.

A zaɓen, Hakeem ya samu kuri'u 33, yayin da Oba ya samu 16. Sauran yan takarar kuma, Alhaji Tajudeen Audu, ya samu kuri'a 10, Sunday Babalola, ya samu kuri'a biyu, sai kuma Khaleel Bolaji da Kale Belgore da suka tashi ba ko ɗaya.

Amma Oba ya kai korafi ga Hedkwatar jam'iyyar SDP ta ƙasa da ke Abuja, hakan ya yi sanadin sake shirya sabon zaɓe.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya ce zai zaɓi wanda zai gaje shi a 2023, ya nemi goyon bayan gwamnoni

A wani labarin kuma kun ji cewa Jam'iyyar SDP Ta Tsayar Da Gogaggen Sanata Takarar Shugaban Kasa a 2023

Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta zabi Sanata Ebenezer Ikeyina a matsayin dan takarar shugaban kasar ta a 2023.

Mike Odunrinde, Shugaban Kwamitin Shirya Taron Jam'iyyar ne ya sanar da hakan a birnin tarayya Abuja bayan zaben fidda gwani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel