Shugaba Buhari ya faɗa mana ɗan takarar da yake so ya gaje shi, Gwamna Sule

Shugaba Buhari ya faɗa mana ɗan takarar da yake so ya gaje shi, Gwamna Sule

  • Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce tabbas shugaban ƙasa ya faɗa musu irin mutumin da yake son ya gaje shi a 2023
  • Sule ya ce Buhari bai gaya musu cikakken sunan ɗan takarar ba, amma ya shaida musu siffofinsa kuma ya ba su dama su yi nazari
  • Gwamnan ya kuma ƙara da cewa Atiku na da babban aiki a gabansa da gamsar da yan Najeriya cewa ya fi ɗan takarar APC

Abuja - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya faɗa wa gwamnonin APC ɗan takarar da yake so yayin da jam'iyya ke fuskantar zaɓen fid da gwani.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a wurin hira da kafar watsa labarai ta Talabijin wato Channels tv cikin shirin su na 'Siyasa a yau' ranar Talata.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya shiga tsakanin shugabannin PDP bayan Atiku ya lashe tikitin takarar shugaban kasa

Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule.
Shugaba Buhari ya faɗa mana ɗan takarar da yake so ya gaje shi, Gwamna Sule Hoto: Gov. Abdullahi Sule Mandate/facebook
Asali: Facebook

Shugaban ƙasa Buhari ya gana da gwamnoni 22 na jam'iyyar APC ranar Talata domin tattaunawa kan zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban kasa da kuma bukatar su cimma matsaya guda.

Daily Trust ta rahoto Gwamna Sule ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Shugaban ƙasa ya ce ɗan takarar maslaha ko ɗan takarar da zamu zaɓa wajibi ya zama karbaɓɓe ga yan Najeriya, wanda ya san ciki da bayan APC, abinda ta kunsa da manufar da take son cimma."
"Ya ƙara da cewa wajibi ya kasance wanda zai iya zuwa dukkan sassan Najeriya kuma a karɓe shi. A kalaman shugaba Buhari ya ce, wajibi mu zakulo mai jinin cin nasara kuma wanda zai iya ɗorawa daga kyawawan ayyukan da APC ta yi."
"Amma idan kuna buƙatar jin sunan wannan ɗan takara to shugaban ƙasa bai faɗa mana ba, ya ba mu siffofinsa ne kuma ya bamu damar mu yi tunani a kai a yan kwanakin nan yayin da ya ke can Spain."

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC sun sa labule bayan Buhari ya faɗa musu matsayarsa kan wanda zai gaje shi a 2023

Gwamnan ya yi tsokaci kan tsayar da Atiku

Haka zalika, gwamna Sule yace bayan lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a PDP, Atiku ba da ɗan takarar APC kaɗai zai fafata ba, da jam'iyyar baki ɗaya zai gwabza a zaɓen da ke tafe.

"Yana da sauran aiki a gaban shi saboda tilas sai ya gamsar da mutane cewa ya fi ɗan takarar APC cancanta da kwarewa ta kowane fanni."

A wani labarin kuma Gaskiya ta Fito: Abin da Tambuwal ya faɗa wa shugaban PDP da wasu yan takara biyu kafin janye wa Atiku

Wasu bayanai da suka fito sun bayyana yadda Tambuwal ya nemi shawarin shugaban PDP da wasu mutum biyu kafin janye wa Atiku.

Wata majiya ta ce gwamnan ya faɗa wa Bukola Saraki, Bala Muhammed, matakin da ya ɗauka kafin zuwa wurin Ayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel