Sanatan APC: Gwamna Wike ya yi kokari, shi ya ci zaben fidda gwani ba Àtiku ba a ra'ayina

Sanatan APC: Gwamna Wike ya yi kokari, shi ya ci zaben fidda gwani ba Àtiku ba a ra'ayina

  • Sanata Orji Kalu ya yi martani a kan sakamakon zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP)
  • Kalu wanda ya kasance jigon jam’iyyar APC ya yi jinjina ga Gwamna Nyesom Wike wanda ya sha kaye a hannun Atiku Abubakar
  • Ya bayyana Gwamna Wike a matsayin jajirtaccen mutum wanda ya yi yaki sosai duk da hade masa kai da aka yi

Shugaban masu tsawatarwa na majalisar dattawa, Orji Kalu, ya jinjinawa tsohon dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, kan zuwa na biyu da ya yi a zaben fidda gwanin jam’iyyar.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, 30 ga watan Mayu, Kalu ya bayyana Wike a matsayin ainahin wanda ya yi nasara a zaben.

Kara karanta wannan

Mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2023 zai iya zama Gwamnan da ya yi takara da shi

Kalu wanda ya kasance jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya ce duk da suna da banbancin ra’ayi da Wike a bangaren siyasa, yana alfahari da gwamnan na jihar Rivers.

Sanatan APC: Gwamna Wike ya yi kokari, shi ya ci zaben fidda gwani ba Àtiku ba a ra'ayina
Sanatan APC: Gwamna Wike ya yi kokari, shi ya ci zaben fidda gwani ba Àtiku ba a ra'ayina Hoto: Senator Orji Uzor Kalu
Asali: Facebook

Ya rubuta a shafin nasa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Koda dai ni jigo ne na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), dole na fadi cewa ina alfahari da kokarin Gwamna Nyesom Wike, jajircewa da karfin gwiwarsa.
“Eh ya sha kaye, amma ya yi gwagwarmaya sosai. Ina taya shi kuma sannan ina jinjinawa taurin ransa a zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP da aka kammala.
“Zan iya cewa Wike ne kawai wanda ya yi nasara a tseren saboda tsallake dukkan kalubale don zama na biyu. Karbi jinjina, Nyesom Wike!"

Shugaban kasa: Nasarar Atiku babban kalubale ne ga APC a 2023 – Orji Kalu

A gefe guda, Orji Kalu, ya bayyana cewa bayyanar Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party(PDP) yasa akwai bukatar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fitar da dan takara daga arewa idan har tana son ci gaba da mulki a 2023.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike: Da Na So, Da Na Tarwatsa Jam'iyyar PDP a Daren Asabar, Hakuri Kawai Nayi

Kalu a cikin wata sanarwa da ya fitar jim kadan bayan ayyana Atiku a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin PDP na ranar Asabar, ya ce ya kamata APC ta dauki dan takara daga arewa maso gabas saboda daga yankin ne Atiku ya fito.

Tsohon gwamnan na jihar Abia ya yi nuni ga zabar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan wanda ya fito daga jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel