Bayan ya bar APC, PDP ta ba Sanatan yankin Shugaba Buhari tikitin neman takara a araha

Bayan ya bar APC, PDP ta ba Sanatan yankin Shugaba Buhari tikitin neman takara a araha

  • Sanata Ahmed Babba Kaita zai sake neman takarar majalisar dattawa na shiyyar Arewacin Katsina
  • Wannan karo ‘Dan majalisar zai tsaya neman kujerar ne a karkashin jam’iyyar hamayya ta PDP
  • Jam’iyyar PDP ta tsaida Babba Kaita ya yi mata takara a zaben 2023, babu wanda ya yi takara da shi

Katsina - Rahoton da mu ka samu daga Katsina Post ya tabbatar da cewa Ahmed Babba Kaita ne zai yi wa jam’iyyar PDP takara a Arewacin jihar Katsina.

Sanata Ahmed Babba Kaita ya yi nasarar lashe zaben zama ‘dan takarar jam’iyyar hamayya ta PDP na ‘dan majalisar dattawa da zai wakilaci yankin Daura.

Jam’iyyar PDP ta tabbatar da Ahmed Babba Kaita a matsayin ‘dan takararta a 2023 bayan zaben gwanin da aka shirya a ranar Litinin, 23 ga watan Mayu 2022.

Kara karanta wannan

‘Dan takara ya fasa rabawa ‘Ya ‘yan PDP Naira Miliyan 92 tun da sun ki zaben shi

Kamar yadda jaridar ta fitar da labari na musamman dazu, Babba Kaita ya samu tikiti ne ba tare da hamayya ba, babu wani ‘dan takara da ya tsaya takara da shi.

Daukacin masu kada kuri’a a zaben tsaida gwani a PDP na shiyyar Arewacin jihar Katsina sun zabi Sanatan mai-ci watau Babba Kaita a matsayin ‘dan takara.

Hukumar zabe mai zaman kanta a kasa watau INEC ta tura wakili da ya sa ido a wajen zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan yankin Shugaba Buhari
Sanata Ahmed Babba Kaita tare da Shugaban kasa Hoto: www.thebridgenewsng.com
Asali: UGC

Haka zalika shugabannin PDP na matakin kasa da sauran ‘yan takarar jam’iyyar na jihar Katsina sun samu halartar wannan zabe da ya gudana cikin zaman lafiya.

An shirya zaben fitar da ‘dan takarar ne a sakatariyar jam’iyyar hamayyar da ke jihar Katsina. Kaita kadai ne wanda bai da abokin adawa wajen takarar Sanata.

Alhaji Salisu Yusuf Majigiri wanda jigo ne a jam’iyyar PDP kuma mai neman takarar gwamna a zaben 2023 ya na cikin wadanda suka samu zuwa wajen zaben.

Kara karanta wannan

2023: Shahararren Mawakin Najeriya ya yi nasarar samun takarar ‘Dan Majalisa a PDP

Babba Kaita ya yi godiya

A jawabin da ya gabatar bayan nasarar da ya samu, Ahmed Babba Kaita ya yi godiya ga ‘ya ‘yan jam’iyyarsa da suka zabe shi da nufin ya yi masu takara a 2023.

Sanata Ahmed Babba Kaita ya yaba da irin kaunar da yake gani a wajen ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP da ya shigo cikinsu bayan ya sauya-sheka daga APC kwanakin baya.

Babba Kaita ya sha alwashin cigaba da kokari wajen kawowa yankin na sa alheran da ke majalisa.

Ahmad Babba-Kaita ya bar APC

Idan za a iya tunawa, a ranar Laraba, 20 ga watan Afrilun shekarar nan ne Ahmad Babba-Kaita ya sanarwar komawa jam’iyyar PDP mai adawa a Kasa da jihar Katsina.

Hakan na zuwa ne bayan sabanin da 'dan majalisar ya samu da jagororin APC na Katsina. Kafin canza shekar, an yi tunanin zai yi takarar gwamnan Katsina a APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel