Zaben fidda gwani: An sanar da wanda ya lashe tikitin takarar gwamnan APC a Sokoto

Zaben fidda gwani: An sanar da wanda ya lashe tikitin takarar gwamnan APC a Sokoto

  • Sakamakon zaben fidda gwani daga jihar Sokoto ya fito, an bayyana sunan Ahmed Aliyu a matsayin wanda ya lashe zabe
  • Wannan na zuwa ne bayan 'yar hatsaniya da aka samu a harabar zaben daga wasu jiga-jigan jam'iyyar APC
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da sanar da sunayen wadanda suka lashe zaben fidda gwani na APC a jihohin kasar nan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Sokoto - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya zama wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar Sokoto, TVC ta ruwaito.

Aliyu, ya samu kuri’u 1,080 daga cikin jimillar kuri’u 1,182 da aka kada a zaben fidda gwani da ‘yan takara shida suka fafata a ciki.

Shugaban kwamitin zaben, Aliyu Kyari, ya ce Ibrahim Gobir ya samu kuri’u 36, Faruk Malami-Yabo ya samu kuri’u 27, sai kuma tsohon ministan sufuri, Yusuf Suleiman ya samu kuri’u 16 da kuri’u 23 da kuma kuri'un da suka lalace.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Umar Bago ya lashe zaben fidda dan takarar gwamnan APC a Neja

Yadda zaben fidda gwanin APC ta kaya a jihar Sokoto
Zaben fidda gwani: An sanar da wanda ya lashe tikitin takarar gwamnan APC a Sokoto | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Kyari ya ce sauran ‘yan takarar sun hada da Abubakar Abdullahi mai kuri’a 1 da Sen. Umar Gada mai kuri’u zifiri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ya bayyana Aliyu ne da mafi yawan kuri’u a matsayin wanda ya yi nasara bisa tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC.

Deliget-deliget da sauran masu ruwa da tsaki sun koka kan tsarin da kuma yadda aka gudanar da zaben fidda gwanin, inji rahoton Vanguard.

Sauran ‘yan takaran dai sun nuna damuwa kan bata kusan sa’a guda a yayin gudanar da zaben.

Ambasada Malami-Yabo, Suleiman da Abubakar sun mika kokensu ga ‘yan kwamitin, inda suka bukaci dukkanin manyan jiga-jigan da ake zargin suna tsoratar da deliget da su fice daga harabar domin tabbatar da an samu daidaito.

An kuma dakatar da ayyukan na tsawon sa'o'i kan muhawarar da ta bullo yayin da 'yan takarar suka yi kira ga kwamitin da ya bi hanyoyin da suka dace.

Kara karanta wannan

Karin bayani: APC ta sanar da wanda ya lashe zaben fidda gwanin gwamna a bauchi

Sokoto: Ƴan Takarar APC Sun Fice Daga Wurin Zaɓen Fidda Gwani a Fusace Bayan Ɗaukewar Wutar Lantarki

A wani labarin, yayin da ake tsaka da zaben fidda gwanin jam’iyyar APC a Jihar Sokoto, akalla ‘yan takarar gwamna guda uku cikin guda 5 ne su ka bar wurin zaben, The Punch ta ruwaito.

Hakan ya biyo bayan rashin wutar lantarki a babban ofishin jam’iyyar na jihar bayan man fetur din injin da ke samar da wutar ya kare.

Wakilin The Punch ya bayyana yadda lamarin ya kai kusan sa’a daya inda wasu ‘yan takarar su ka nemi a dakata da zaben har a dawo da wuta amma aka ki sauraronsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel