‘Dan takara ya fasa rabawa ‘Ya ‘yan PDP Naira Miliyan 92 tun da sun ki zaben shi

‘Dan takara ya fasa rabawa ‘Ya ‘yan PDP Naira Miliyan 92 tun da sun ki zaben shi

  • Hon. Shehu Usman ABG ya nemi PDP ta tsaida shi a matsayin ‘dan takarar majalisar wakilan tarayya
  • ‘Dan siyasar bai iya samun tikitin zaben 2023 ba, ya sha kashi a hannun sabon shiga jam’iyyar PDP
  • Hakan ta sa ya ajiye maganar rabawa masu tsaida ‘dan takaran PDP kudin da ya yi masu alkawari

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Shehu Usman ABG ya janye alkawarin da ya yi wa ‘ya ‘yan jam’iyya ganin ya gaza samun takara a zaben fitar da gwanin da aka gudanar.

Daily Trust ta ce Shehu Usman ABG ya nemi samun takarar ‘dan majalisar wakilan tarayya na mazabar Kaduna ta Arewa, amma bai iya yin nasara ba.

Kamar yadda aka ji labari, Hon. Shehu Usman ABG ya sha kashi ne a hannun Hon. Samaila Suleiman wanda shi ne a kan wannan kujera tun 2015.

Kara karanta wannan

2023: Shahararren Mawakin Najeriya ya yi nasarar samun takarar ‘Dan Majalisa a PDP

Kafin a shiga zaben na ranar Lahadi, Shehu ABG ya yi alkawari zai bada Naira miliyan 2.5 ga kowane mai kada kuri’a wajen zaben tsaida ‘dan takara.

Makomar ‘dan takarar Kaduna ta Arewa a PDP ta na hannun wadannan ‘ya ‘yan jam’iyya su 37. A karshe, ana zargin sun bi kudi, su ka zabi wani dabam.

N92.5m sun koma aljihun Hon.

Da a ce ABG ne ya yi galaba a zaben, ya samu tutar takara a karkashin jam’iyyar adawar, zai ba wadanda suka zabe shi abin da ya kai Naira miliyan 92.5.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Yan Majalisa
'Yan majalisar wakilan tarayya Hoto: @HouseNgr
Asali: Facebook

Tun da mafi yawan ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP ba su ba shi kuri’unsu ba, ‘dan siyasar ya tattara kudinsa ya koma da su gida, ba tare da ya ba kowa ba.

Samaila Suleiman ya ci zabe

Rahoton da jaridar ta fitar ya bayyana cewa Honarabul Samaila Suleiman da ya samu tikitin ya kashe tsakanin N3.5m zuwa N4m a kan masu tsaida zabe.

Kara karanta wannan

Mutum 5 kacal ke neman takarar shugaban Najeriya tsakani da Allah inji ‘Dan takaran APC

Ana zargin ‘dan majalisar mai-ci ya kashe abin da ya fi Naira miliyan 130 domin ya nemi tazarce. Bai dade da dawowa PDP daga APC mai mulkin jihar ba.

Wasu daga cikin ‘ya ‘yan PDP a karamar hukumar Kaduna ta Arewa sun koka a kan yadda aka saida takara ga wadanda kwanan nan suka sauya-sheka.

Sulaiman ya samu kuri’u 20, ABG ya tashi da 14, sai kuma Adam Namadi Sambo ya samu 2.

Bello El-Rufai zai yi takara

A baya kun samu rahoto cewa da alama Bello El-Rufai ne wanda jam'iyyar APC za ta ba takarar majalisar wakilan tarayya a yankin Kaduna ta Arewa a 2023.

Samaila Suleiman mai wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisa ya bar APC ne saboda ya lura Bello El-Rufai yana harin kujerarsa, don haka da wahala ya kai labari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel