LP, NNPP, Jam’iyyu 4 da Peter Obi zai iya komawa kafin zaben 2023 bayan watsi da PDP

LP, NNPP, Jam’iyyu 4 da Peter Obi zai iya komawa kafin zaben 2023 bayan watsi da PDP

  • A ranar Laraba, 25 ga watan Mayu, 2022 ne aka ji Peter Obi ya bada sanarwar cewa ya fice daga PDP
  • Masu nazarin siyasa su na ganin sauya-shekar Obi za ta iya nakasa jam’iyyar PDP a zaben 2023
  • Ana tunanin tsohon Gwamnan zai nemi wata jam’iyyar hamayya da zai shiga domin yin takara

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ana zargin Obi ya bar PDP ne a dalilin sabanin da ya samu da shugabannin jam’iyyar na kin kafa kwamitin da za su shirya zaben tsaida gwani a jiharsa ta Anambra.

Haka zalika jam’iyyar hamayyar ta bar kofar takara a bude, a maimakon ta bada dama ‘dan takarar shugaban kasa na zaben 2023 ya fito daga kudancin Najeriya.

A wannan rahoto da za a karanta, Legit.ng Hausa ta yi nazarin halin da Peter Obi ya shiga, da jam’iyyar da ake tunanin ‘dan siyasar zai runguma gabanin zabe.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bayan janyewa daga takarar shugaban kasa, Peter Obi ya fice daga PDP

Wace jam’iyya Obi zai koma?

1. APGA

A shekarar 2018 ne Peter Obi ya yi watsi da APGA, jam’iyyar da ta fara fito da shi har ya zama gwamna na tsawon shekaru takwas tsakanin 2007 da 2015.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban APGA, Victor Oye ya taba cewa Obi ba zai sake zama komai a siyasa ba har sai idan ya dawo jam’iyya. APGA ta na da gwamna daya, jihar Anambra.

Peter Obi a PDP
Peter Obi wajen yakin neman kuri'a Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

2. LP

Wata jam’iyya da tsohon ‘dan takarar mataimakin shugaban kasar zai iya shiga ita ce jam’iyyar Labor Party. Wata majiya ta tabbatar da wannan rade-radin.

Jam’iyyar LP ta fi APGA karbuwa a wajen kudu maso gabashin Najeriya. Sai dai LP ba ta rike da wata jiha a halin yanzu tun da Olusegun Mimiko ya bar mulki.

3. SDP

Akwai masu tunanin tsohon gwamnan zai sauya-sheka zuwa jam’iyyar hamayya ta SDP. The Nation ta ce babu mamaki ya jarraba sa’arsa a wata jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Kaduna, surukin Buhari bai aminta da deleget din jam’iyyar ba

Zuwa yanzu SDP ba ta da ‘dan takarar shugaban kasan da ya fi Obi shahara, amma ana tunanin ta na shirin karbar wadanda za su iya barin APC kwanan nan.

4. NNPP

Wani zabi da Peter Obi yake da shi a 2023 shi ne ya shiga jam’iyyar adawa ta NNPP. Ana ganin tikitin Obi da Rabiu Kwakwanso zai tada hankalin APC da PDP.

Sai dai zai yi wahala Sanata Rabiu Kwakwanso ya mika tikitin shugaban kasa ga Obi, ganin cewa shi ya babbako jam’iyyar tun lokacin Obi bai kai ga canza gida ba.

Jonathan zai yi takara?

A jiya aka ji labari tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi zama da Malam Mamman Daura a gidansa a yayin da ake shirin zaben tsaida gwani a APC.

Ana tunanin makasudin zaman bai wuce burin wasu na ganin Jonathan ya karbi mulki ba. A halin yanzu kafar Jonathan daya ta na cikin jam'iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

Bayan ya bar APC, PDP ta ba Sanatan yankin Shugaba Buhari tikitin neman takara a araha

Asali: Legit.ng

Online view pixel