PDP ta tsaida ‘Yan takarar Gwamna 2 a jihar Kano, ‘Ya ‘yan Wali da Abacha sun samu tikiti

PDP ta tsaida ‘Yan takarar Gwamna 2 a jihar Kano, ‘Ya ‘yan Wali da Abacha sun samu tikiti

  • Sadiq Wali ya zama ‘dan takarar jam’iyyar PDP a jihar Kano na tsagin su Sanata Bello Hayatu Gwarzo
  • Su kuma bangaren Shehu Wada Sagagi sun tsaida Mohammed Abacha a matsayin ‘dan takararsu
  • Jam’iyyar PDP da ke tsundume cikin rikicin gida ta samu ‘yan takarar Gwamna biyu a zaben 2023

Kano - Sadiq Wali wanda ‘da ne a wajen Ambasada Aminu Wali da ‘dan tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha, Mohammed Abacha sun samu tikitin PDP.

Rahoton da ya fito daga Daily Trust ya bayyana cewa Mohammed Abacha ne ya yi nasara a zaben da bangaren jam’iyyar PDP na Shehu Wada Sagagi suka shirya.

A gefe guda kuma, Sadiq Wali shi ne wanda ya samu nasara a zaben tsaida gwanin da ‘yan tawaren PDP da ke tare da Bello Hayatu Gwarzo suka gudanar.

Kara karanta wannan

2023: Dasuki ya samu takarar Majalisa a PDP, yana goyon bayan Tambuwal a kan Atiku

Mutanen Sanata Bello Hayatu Gwarzo sun yi zabensu ne a filin Sani Abacha Youth Centre yayin da tsagin Sagagi suka shirya zaben na su a sakatariyar jam’iyya.

Sadiq Wali ya doke su Dangwani

Sadiq Wali ya rike Kwamishinan harkar ruwa a gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje. Sai a watan Afrilun nan ya ajiye aikinsa bayan an kada gangar siyasar 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da yana ‘dan jam’iyyar hamayya, Gwamna Ganduje ya nada Wali a matsayin Kwamshina. Hakan ta sa ake zargin tsaginsu da yi wa APC aiki a zaben 2019.

PDP ta tsaida ‘Yan takarar Gwamna a Kano
Wasu Masu takarar Gwamnan Kano a PDP Hoto: muaz.magaji
Asali: Facebook

Mahaifinsa shi ne tsohon Ministan tarayya kuma jigon PDP na kasa, Ambasada Aminu Wali.

A gefe guda kuma ‘yan tawaren su na zargin Shehu Sagagi yana yi wa Rabiu Kwankwaso aiki ne a PDP bayan shi da mutanensa duk sun sauya-sheka zuwa NNPP.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya sha kashi a zaben ‘dan takarar Gwamnan Kaduna, ya tsira da kuri’u 2

Mohammed Abacha wanda ya ke ikirarin shi ne 'dan takara na ainihi, yana cikin 'ya 'yan Marigayi Sani Abacha wanda ya mulki Najeriya daga 1993-1998.

Sakamakon zaben 'yan taware

Daily Nigerian ta ce Bunmi Adu wanda ya jagoranci zaben ya bada sanarwar cewa Sadiq Wali ya samu kuri’u 455 a zaben, sannan Ibrahim Amin Little ya samu 333.

Tsohon hadimin Rabiu Kwankwaso, Dr. Yunusa Dangwani shi ne ya zo na uku da kuri’u 276.

Yusuf Dambatta wanda shi ma ya fice daga tsagin Kwankwasiyya, ya yi zamansa a PDP ya samu 182. Muaz Magaji ya ci kuri'a 25, sai Mustapha Getso ya kare da 20.

Garo ba zai bar APC ba

A farkon makon nan ne mu ka kawo maku labari cewa Hon. Murtala Sule Garo ya tabbatar da cewa yana nan daram a cikin jam’iyyar APC mai mulkin jihar Kano.

Akasin jita-jitar da ake ta yi a jihar Kano, Murtala Sule Garo ya ce bai sauya sheka zuwa adawa ba. Garo ne wanda zai yi wa APC takarar mataimakin gwamna a 2023.

Kara karanta wannan

Rikicin gidan PDP ya jagwalgwale a Kano, an rasa gane wadanda za su yi takara a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel