Rudani: Sanatan APC Goje ya tura wasika ga PDP bayan ganin sunansa a jam'iyyar

Rudani: Sanatan APC Goje ya tura wasika ga PDP bayan ganin sunansa a jam'iyyar

  • Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya ya fusata, ya aike da sako ga jam'iyyar PDP kan sanya sunansa cikin 'yan takararta
  • Ya ce sam ba zai lamunci wannan bata suna ba, kuma lallai zai dauki mataki na doka a kan lamarin
  • Rahotanni dai sun bayyana cewa, an ga sunan Goje a cikin wani jerin sunayen 'yan takarar sanata a jam'iyyar PDP

Abuja - Sanatan APC mai wakiltar Gombe ta tsakiya, Mohammed Danjuma Goje, ya rubutawa shugaban PDP na kasa Iyorchia Ayu wasika kan sanya sunansa a cikin wadanda suka halarci zaben fidda gwanin jam’iyyar adawan a jihar Gombe.

Cikakken suna da hoton Goje sun bayyana a takardar PDP tare da wasu mutanen da aka ce suma sun halarci zaben fidda gwani da aka gudanar a ranar 23 ga watan Mayun 2022.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bayan janyewa daga takarar shugaban kasa, Peter Obi ya fice daga PDP

Sanata Goje ya ce shi cikakken dan APC ne babu surki
Zan dauki mataki: Sanata Goje ya kai wasika ga Ayu kan batun shiga harkar PDP | Hoto: leadership.ng
Asali: Twitter

Sai dai dan majalisar a cikin wata wasika da ya aikewa shugaban jam'iyyar PDP ta hannun lauyansa, Paul Erokoro (SAN), ya sake nanata cewa shi cikakken dan APC ne, wanda aka zabe shi a matsayin Sanata sau biyu.

Ya nanata cewa bai koma PDP ko wata jam’iyyar siyasa ba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce gama sunansa a cikin ‘yan takarar Sanata na PDP, wani shiri ne na bata-gari, wadanda suke neman bata masa suna da kimarsa.

Don haka Goje ya sha alwashin daukar matakin doka a kan wadanda suka yi yunkurin lalata alkadarin siyasarsa.

Yana Sanatan APC amma sunan Danjuma Goje ya bayyana wajen zaben fidda gwanin PDP

A baya mun kawo rahoton da ke cewa, wakilan zaben shugaba wadanda akafi sani da deleget na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Gombe sun ga abin mamaki ranar Litnin wajen zaben fidda gwani.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Tashin hankali yayin da PDP ta dage zaben fidda gwani bayan barkewar rikici

Yayin da suka shiga kada kuri'unsu, sai suka ga Sanatan APC mai wakiltar Gombe ta tsakiya, Danjuma Goje, cikin jerin yan takaran, rahoton Leadership.

Zaku tuna cewa an yi rade-radin Sanata Danjuma Goje zai sauya sheka daga APC zuwa PDP sakamakon rashin jituwar dake tsakninsa da Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa Yahaya.

Tuni dai uwar jam'iyyar APC ta shirya zaman sulhu tsakanin jiga-jigan siyasan kuma hakan ya hana Danjuma Goje komawa PDP.

Amma a ranar Litinin yayi zaben fidda gwanin PDP, sunan Danjuma Goje ya bayyana cikin yan takara.

Siyasar Gombe ta sauya, amma ba lallai Goje ya koma PDP ba, duk zai iya komawa

Mai sharhi kuma masanin siyasar jihar Gombe daga jami'ar jiha, Mallam Muhammad B. Abdulazeez, ya shaidawa wakilinmu cewa:

"Abu ne mai matukar wahala a ce Goje ya yi wasa da kujerarsa, kuma duba da siyasarsa, mutum ne mai jama'a daga mazabarsa ta sanata da ma wasu mazabu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Gwamnonin APC sun shirya tsaf domin zaban dan takarar da zai gaji Buhari

"Don haka, komawarsa PDP idan da gaske ne, ba za ta buta ba, kuma ba zai fito ya kalubalanci shugaban PDP Ayu a wata wasika ba ta hannun lauyansa.
"Ko da yake, idan Goje zai koma PDP ba komai bane, saboda daga cikinta ya fito, kuma ya taka rawar gani, kuma akwai alamar masoyansa za su iya zabarsa a PDP ganin yadda wasu ke koka mulkin APC a jihar.
"Karshe, a nawa ganin, Goje da APC ko PDP, idan bai bar siyasa ba, to zai taka rawar gani a siyasar jihar Gombe."

A wani labarin na daban kuma, tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Muhammad Danjuma Goje ya fara rabon babura masu kafa uku (Keke Napep) 500 da babura 1000 a mazabarsa a gundumar Gombe ta tsakiya.

A cewar Goje, hakan na daga cikin kokarinsa na yaki da talauci tare da karfafawa talakawan mazabar sa da samar musu da aikin yi, kamar yadda Legit.ng ta samo.

Kara karanta wannan

2023: Shahararren Mawakin Najeriya ya yi nasarar samun takarar ‘Dan Majalisa a PDP

Sanatan na jam’iyyar APC, ya kuma bayyana cewa ya dauki matakin ne domin samar da ayyukan yi ga matasa a yankinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel