Basu da alkawari: Ina rokon Allah ya hana dan siyasa zama magajin Buhari – Mai neman takarar shugaban kasa

Basu da alkawari: Ina rokon Allah ya hana dan siyasa zama magajin Buhari – Mai neman takarar shugaban kasa

  • Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya bayyana cewa yana ci gaba da rokon Allah kan kada ya bari dan siyasa ya zama shugaban kasar Najeriya na gaba
  • Umahi wanda ke son ya gaje Buhari a zabe mai zuwa, ya ce yan siyasa basu da alkawari kuma sun gazawa yan Najeriya
  • A cewar dan takarar, ya kamata shugaban kasa na gaba ya kasance injiniya kamar sa wanda zai mayar da hankali wajen gina kasar

Gwamnan jihar Ebonyi kuma mai neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Dave Umahi, ya ce yana rokon Allah kada ya ba dan siyasa nasarar zama shugaban Najeriya na gaba.

Umahi ya ce yan siyasa na daukar alkawara duk lokacin da zabe ya zo sannan sai su ki cika su, yana mai cewa Najeriya baya bukatar irin wannan shugaba a wannan karon, tahoton Punch.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya bayyana irin yadda yake matukar son gaje Buhari, ya ce ba wasa yake ba

Basu da alkawari: Ina rokon Allah ya hana dan siyasa zama magajin Buhari – Mai neman takarar shugaban kasa
Basu da alkawari: Ina rokon Allah ya hana dan siyasa zama magajin Buhari – Mai neman takarar shugaban kasa Hoto: Dave Umahi
Asali: UGC

Ya bayyana cewa a matsayinsa na injiniya, ya fi cancanta don jagorantar kasar nan.

Gwamnan ya kuma jaddada cewa bai kamata kudi ya yi tasiri kan wanda ya kamata mutane su zaba ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Channels TV ta kuma rahoto cewa mai neman takarar kujerar shugabancin kasar, ya ce ya kamata shugaban kasa na gaba ya kasance injiniya kamar sa wanda zai mayar da hankali wajen gina kasar.

A cikin wata takarda da aka gabatar a ranar Lahadi, gwamnan ya ce:

“A zahirin gaskiya, Ina ci gaba da addu’an cewa Allah ba zai kawo dan siyasa ba. An sha yin alkawara a baya kuma sun gaza. Ba za mu dogara da alkawara ba. Na tsani jin alkawara.
“Ni injiniya ne kuma ba a taba ba injiniyoyi damar jagorantar kasar nan ba. Muna da ababen more rayuwa da suka rube a kasar nan. Matsayata shine cewa su bari injiniyoyi, wadanda nake kallo a matsayin masu hallita, su gina kasar nan. Bayan nan, Za mu mika mulki ga yan siyasa. A yanzu, muna bukatar kwararre.

Kara karanta wannan

Lalong: Abin Da Yasa Ba Zan Goyi Bayan Ɗan Takarar Shugaban Kasa Daga Arewa Ba a APC

“Kasar mu ta shiga mataki na tsananin takaici inda muka yarda cewa kudi shine amsar komai. Na san wani da ke cewa abun da kudi ba zai iya yi ba, karin kudi zai iya yinsa. Da yanayin da kasarmu ke ciki a yanzu, ya kanata mu dunga magana ne kan wanda zai iya wannan aiki ba wai kan nawa kake da shi ba. Wani ya tambaye ni mai ya banbanta ni da saura? Kiran Allah ne da kuma abun da muka yi nasarar cimmawa ta hanyar alfarmar Ubangiji.”

Da yake magana kan shawarar cewa ya kamata yan takarar shugaban kasa daga kudu maso gabas su cimma maslaha don bunkasa damar da yankin ke da shi, Umahi ya ce:

“Babu bukatar cimma yarjejeniya. Da suka ce ya kamata yan Igbo su hade, na ci gaba da fada masu cewa babu wani abu mai kama da haka. Igbo ba za su zama shugaban kasa ga yan Igbo kawai ba. Muna da adadin na yan takara masu kyau daga kudu maso gabas da yan Najeriya za su iya zaba a cikinsu.”

Kara karanta wannan

Ba Ni Da Kuɗi Amma Ina Tausayin Ƴan Najeriya, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC, Fayemi

Umahi ya kuma jadadda cewa jihar Ebonyi ba za ta kasance cikin Biyafara ba, yana mai cewa Ebube Agu sun taimaka wajen inganta tsaro a jihar. Ya kara da cewa:

“Wannan fafutuka da haramtacciyar kungiyar IPOB ke yi shirme ne, a gani na, saboda koda zai kasance Biyafara, Ebonyi ba za ta kasance cikin Biyafra ba. Na sha fada kuma zan ci gaba da fadi kuma babu wanda zan ba hakuri.”

Da yake magana kan rashin tsaro a kudu maso gabas da kasa baki daya, gwamnan ya daura alhakin kan rashawa, sakacin matasa da siyasa.

Yan takarar shugaban kasa na APC daga kudu maso gabas sun shiga ganawar sirri

A wani labarin, mun ji cewa gabannin zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki wanda za a yi a ranar Lahadi mai zuwa, yan takara daga yankin kudu maso gabas suna cikin wata ganawa ta sirri a yanzu haka.

Kara karanta wannan

Manjo Hamza Al-Mustapha: Ina gaje Buhari zan tare a dajin Sambisa saboda dalilai

An fara ganawar wacce ke gudana a gidan tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, da ke Abuja, da misalin karfe 3:45 na yamma.

Koda dai ba a riga an sanar da jama’a manufar ganawar ba, wani hadimin Okorocha wanda ya nemi a sakaya sunansa ya fadama jaridar Daily Trust cewa ganawar ya karkata ne kan yadda Za a fitar da dan takarar maslaha a tsakanin yan takarar yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng