Da dumi-dumi: Yan takarar shugaban kasa na APC daga kudu maso gabas sun shiga ganawar sirri

Da dumi-dumi: Yan takarar shugaban kasa na APC daga kudu maso gabas sun shiga ganawar sirri

  • Masu neman takarar shugaban kasa na APC daga yankin kudu maso gabas sun shiga ganawar sirri gabannin zaben fidda gwani da za a yi a mako mai zuwa
  • Koda dai ba a san manufar ganawar tasu ba a yanzu haka, ana ganin suna kokarin fitar da dan takarar maslaha ne a tsakaninsu
  • Ganawar na gudana ne a gidan tsohon gwamnan jihar Imo kuma sanata mai ci, Sanata Rochas Okorocha a Abuja

Abuja - Gabannin zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki wanda za a yi a ranar Lahadi mai zuwa, yan takara daga yankin kudu maso gabas suna cikin wata ganawa ta sirri a yanzu haka.

An fara ganawar wacce ke gudana a gidan tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, da ke Abuj, da misalin karfe 3:45 na yamma.

Kara karanta wannan

Buhari ya zalunce ku, idan na zama shugaban ƙasa da ku zan tafi, Tambuwal ga yan kudu maso gabas

Da dumi-dumi: Yan takarar shugaban kasa na APC daga kudu maso gabas sun shiga ganawar sirri
Da dumi-dumi: Yan takarar shugaban kasa na APC daga kudu maso gabas sun shiga ganawar sirri Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Koda dai ba a riga an sanar da jama’a manufar ganawar ba, wani hadimin Okorocha wanda ya nemi a sakaya sunansa ya fadama jaridar Daily Trust cewa ganawar ya karkata ne kan yadda Za a fitar da dan takarar maslaha a tsakanin yan takarar yankin.

Hadimin Okorocha ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Kudu maso gabas ta dauki batun sanar day shugaban kasa a wannan karon da muhimmanci. Hakan ya sa shugabanninmu kimanin kiran wannan taron domin cimma matsaya guda. Ina iya tabbatar maku da cewa yankin zai gabatar da dan takarar da zai samu karbuwa a kasa gaba daya.”

Wadanda suka halarci ganawar sun hada da tsohon ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu; tsohon karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba; tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani; Sanata Rochas Okorocha da yar takara mace daya tilo, Uju Ohanenye.

Kara karanta wannan

Tambuwal da Gwamnoni 9 masu neman mulki su na kashe miliyoyi duk rana a hayar jirgi

A daidai lokacin has kawo wannan rahoton, gwamnan jihar Ebonyi wanda shima yana hararar kujerar, Dave Umahi bai isa wajen taron ba, rahoton The Nation.

Daily Trust ta rahoto cewa a yanzu haka, jam’iyyar APC mai mulki tana duba yiwuwar fitar da dan takarar maslaha cikin wadanda suka yanki fom din takarar shugaban kasa.

SDP ta bayyana abun da za ta duba kafin ta baiwa Tinubu da sauran yan siyasa tikitinta

A wani labari na daban, jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ta gindaya wasu sharudda kafin ta amince da jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da jiga-jigan sauran jam’iyyun siyasa da ka so yin amfani da dandamalinta.

Mukaddashin shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Cif Supo Shonibare, ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a gefen taron jam’iyyar da aka yi a Lagas.

Kara karanta wannan

Rikicin siyasar Kano: Garo na shirin barin APC duk da zabarsa da aka yi ya gaji Gawuna

Daily Trust ta rahoto cewa ana rade-radin wasu yan takarar APC da na PDP na iya sauya sheka daga jam’iyyunsu zuwa wata idan suka gaza samun tikitin takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel