Magudi akayi min a 2019, ni na lashe zabe: Atiku Abubakar

Magudi akayi min a 2019, ni na lashe zabe: Atiku Abubakar

  • Alhaji Atiku Abubakar ya ce wannan karon ba zai yarda a yi masa magudi kamar yadda akayi masa a 2019 ba
  • Shahrarren dan siyasan yace jam'iyya mai mulki ta yi amfani da karfin ofis wajen kwace nasara hannunsa
  • Jam'iyyar PDP ta dage ranar gudanar da zaben tsayar da gwanin dan takarar shugaban kasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma mai neman kujeran shugaba a 2023 karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya jaddada cewa shi ya lashe zaben shugaban kasa a 2019.

Atiku yace kawai jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi amfani da karfin mulki wajen kwace nasarar daga hannunsa.

Ya kara da cewa sam ba zasu taba yarda a sake musu irin wannan a zaben 2023 idan jam'iyyar PDP ta bashi tikiti.

Kara karanta wannan

Ba Ni Da Kuɗi Amma Ina Tausayin Ƴan Najeriya, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC, Fayemi

Magudi akayi min a 2019, ni na lashe zabe: Atiku Abubakar
Magudi akayi min a 2019, ni na lashe zabe: Atiku Abubakar
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atiku ya bayyana hakan yayinda ya hadu da deleget din jihar Kaduna a sakatariyar jam'iyyar da daren Talata, rahoton Leadership.

Ya bukaci deleget din Kaduna su kada masa kuri'a kamar yadda suka yi a zaben 2018, ya yi alkawarin ba zai basu kunya ba.

Ya tabbatar musu da cewa ba karamin taimakawa Najeriya zai yi ba idan ya zama shugaban kasa.

Yace:

"Ni na lashe zaben 2019 amma aka yi min magudi, kamar yadda aka muku magudi a Kaduna ta hanyar amfani da karfin mulki, amma ba zamu bari hakan ya sake faruwa ba a 2023."
"Saboda haka ina kira ga ku zabi shugabannin kwarai, idan na samu tikitin jam'iyyar kuma na samu nasara a 2023, zan hada kan yan Najeriya."

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi, a nashi jawabin yace lallai su suka lashe zabe a 2019 amma aka hanasu.

Kara karanta wannan

Manjo Hamza Al-Mustapha: Ina gaje Buhari zan tare a dajin Sambisa saboda dalilai

Atiku ya lissafa jihohi 5 da yake zargin APC ta sace masa kuri’u a 2019

Legit Hausa ta zakulo jerin jihohi biyar da dan siyasar wanda ya kasance haifaffen jihar Adamawa ya zargi APC da sace masa kuri’u, ga su kamar haka:

1. Jihar Katsina

2. Jihar Kano

3. Jihar Kaduna

4. Jihar Borno

5. Jihar Yobe

Asali: Legit.ng

Online view pixel