Gwamna Tambuwal: 'Yan Najeriya a Takure Su Ke a Mulkin Buhari

Gwamna Tambuwal: 'Yan Najeriya a Takure Su Ke a Mulkin Buhari

  • Gwamnan Jihar Sokoto kuma dan takarar shugaban kasa karkashin PDP, Aminu Waziri Tambuwal ya zargin cewa ‘yan Najeriya suna cikin takura a mulkin Buhari
  • Ya bayyana hakan ne a Jihar Legas yayin da ya samu ganawa da wakilan jam’iyyar PDP sakamakon yadda zaben fidda gwanin jam’iyyar ya ke kara matsowa
  • A cewarsa, kada ‘yan Najeriya su kara yin babban kuskure, su zabi wanda su ka san ya na da damar kawo gyara da kuma cire Najeriya da halin kangi

Legas - Aminu Waziri Tambuwal, gwamnan Jihar Sokoto kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ya yi zargin cewa ‘yan Najeriya su na rayuwa cikin kunci karkashin mulkin Buhari

Daily Trust ta ruwaito cewa ya fadi hakan ne yayin da ya gana da wakilan jam’iyyar PDP kasancewar zaben fidda gwanin jam’iyyar ya na ta matsowa.

Kara karanta wannan

Saraki ya bayyana ainahin abun da ya haddasa rashin tsaro a Najeriya

Gwamna Tambuwal: 'Kebura' Ƴan Najeriya Ke Sha a Mulkin Buhari
Gwamna Tambuwal: 'Yan Najeriya Cikin Takura Suke Rayuwa a Mulkin Buhari. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya shawarci ‘yan Najeriya da su kiyaye gwajin shugabanci, su zabi wanda su ka san ya na da gogewar da zai iya dawo da Najeriya cikin yanayi mai kyau.

Tambuwal Ya ce Buhari ya takura Najeriya

Ya ce hakan ya na bukatar maza da mata su bayar da goyon baya ga wanda ya fi cancanta don dawo da Najeriya kan tafarki na daidai kamar yadda Daily Trust ta nuna.

A cewarsa:

“Babban aiki ne wanda ya ke bukatar bukatar gogewa kuma bai dace mu yi kuskuren gwada wani da shugabancin kasar nan ba a karo na biyu.
“Ba a gwajin shugabanci in har mutum ya taba shugabantar kasa bai taba rike mulki a lokacin demokradiyya ba. Eh Shugaba Muhammadu Buhari ya taba rike kujerar gwamna, Ministan fetur da kuma shugaban kasa amma ba a zabe shi ba lokacin demokradiyya.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Ni nafi cancanta na gaji Buhari, in ji Saraki

“Don haka bai san yadda ake tafiyar da shugabanci a demokradiyyance ba. Hakan ya sa bai san yadda zai bullowa shugabancin Najeriya ba kuma kasar duk ta takura saboda shi.”

Ya nemi su duba halayya da cancanta wurin zaben dan takara

Ya shawarci wakilan jam’iyyar akan kada su sadaukar da nan gaban yaransu wurin zaben dan takarar da bai cancanta ba, inda ya ce su kula kwarai yayin kada kuru’unsu.

Tambuwal, wanda tsohon kakakin majalisar wakilai nr ya kwatanta kansa a matsayin gadar da ke tsakanin tsofaffi da yara hakan zai ba shi damar fahimtar mummunan yanayin da kowa ya ke ciki.

A cewarsa:

“Nan ne cibiyar fifiko, don haka ya cancanta ku zabi mai fifiko. Ku kula kwarai yayin zabe a ranar 28 da 29 ga watan Mayu.
“Ku yi bincike akan sauran ‘yan takara daga nan ku san abin yi. Hakan zai ba ku damar zaben wanda ya cancanta don kawo gyara a kasar nan.

Kara karanta wannan

2023: Saura kwana 10 zabe, an shiga yamutsi a PDP game da wanda za a tsaida takara

“Ba a batun yankin da mutum ya fito ba. A’a kamata ya yi ka kalla halayya, jajircewa, cancanta da kuma ganin ko ya dace ka yarda da mutum. Idan ka yi kuskuren bayar da shugabanci ga wanda bai cancanta ba, shikenan komai zai lalace.
“Don haka ya dace ku yi nazari mai kyau kuma ku yi tunani mai zurfi kafin tsayar da dan takarar jam’iyyar PDP wanda zai iya lashe zabe gaba daya.”

Shugaban jam’iyyar na Jihar Legas ya yi masa alkawarin za su mara masa baya

Ya ci gaba da bayyana gogewarsa inda ya ce ya yi shekaru 30 a matsayin dan majalisar wakilai tare da mazabu 360 da ke kasar nan a lokuta daban-daban a matsayin mamba, shugaban marasa rinjaye, mataimakin bulaliyar majalisa da kuma kakakin majalisar wakilai.

Ya ce ya san matsalolin kasar nan a yadda su ke. Akwai bukatar dagewa da kuma zage damtse wurin ganin kasar nan ta bunkasa.

Kara karanta wannan

Ku Amshi Kuɗin Ƴan Takara Idan Su Baku Amma Ku Yi Zaɓe Da Hikima, Peter Obi

Shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Legas, Mr Philips Aiwoji ya kada baki ya ce:

“Mun sani kuma da yardar Ubangiji za mu mara maka baya.”

Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel