Saraki ya bayyana ainahin abun da ya haddasa rashin tsaro a Najeriya

Saraki ya bayyana ainahin abun da ya haddasa rashin tsaro a Najeriya

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Buko Saraki ya yi tsokaci kan tarin matsalolin da suke addabar kasar nan
  • Saraki ya bayyana cewa rashin sanin makasar jagoranci shine babban abun da ke haddasa rashin tsaro a Najeriya
  • Ya bayyana cewa akwai bukatar a yi abun da ya kamata domin tsamo kasar daga kangin da take ciki a 2023

Taraba - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa rashin sanin makamar shugabanci shine tushen rashin tsaro a fadin kasar.

Saraki wanda ke neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin inuwar PDP, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a garin Jalingo, babbar birnin jihar Taraba lokacin da ya gana da deleget na jam’iyyar a jihar, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Ni nafi cancanta na gaji Buhari, in ji Saraki

Saraki ya bayyana ainahin abun da ya haddasa rashin tsaro a Najeriya
Saraki ya bayyana ainahin abun da ya haddasa rashin tsaro a Najeriya Hoto: The Cable
Asali: UGC

Ya yi bayanin cewa kasar ta fuskanci abubuwa da dama a cikin shekarun nan ya kamata 2023 ya zama lokacin ceto ta.

Jaridar Guardian ta rahoto cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ba za mu sake samun shugabannin gobe irin wadanda muke da su ba a yau. 2023 ita ce makomar kasar nan da 'ya'yanmu.
“Kasar nan ta rabu sosai kuma ba za mu yarda mu yi amfani da son rai wajen kada kuri’a ba.
“Ya zama dole mu yi abun yadda ya kamata saboda wadanda suka mutu a kan laifin da ba nasu ba.
“Mun sha fama sosai a kasar nan kuma ya zama dole mu samu wadanda suka cancanta don ceto Najeriya.”

Saraki ya ci gaba da fada ma deleget din cewa shi kadai ne dan takarar da ya fito manufa don magance matsalar Najeriya.

Kara karanta wannan

‘Dan takaran Shugaban kasa ya ce zai nemawa mutum miliyan 20 aiki ranar da ya karbi mulki

'Dan takarar PDP ya fadi abin da ya sa Buhari ya gagara gyara Najeriya yadda ake sa rai

A wani labarin, dan takarar shugaban Najeriya kuma gwamnan Bauchi, Bala Abdulqadir Mohammed yana ganin Muhammadu Buhari bai fahimci siyasa ba.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Lahadi, 16 ga watan Mayu 2022, da ya nuna cewa Bala Abdulqadir Mohammed ya kai ziyara zuwa jihar Katsina.

Sanata Bala Abdulqadir Mohammed ya ziyarci jihar shugaban kasar ne da nufin samun goyon bayan ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a zaben fitar da 'dan takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel