Ku Amshi Kuɗin Ƴan Takara Idan Sun Baku Amma Ku Yi Zaɓe Da Hikima, Peter Obi

Ku Amshi Kuɗin Ƴan Takara Idan Sun Baku Amma Ku Yi Zaɓe Da Hikima, Peter Obi

  • Mista Peter Obi, tsohon gwamnan Jihar Abia kuma dan takarar shugaban kasa a PDP ya umurci deleget su karbi kudi idan an ba su
  • Obi ya yi wannan jawabin ne yayin ganawarsa da deleget na Jihar Kaduna amma ya ce kada su bari kudin da suka karba ya sa su ki zaben wanda suke son zaba
  • Dan takarar shugaban kasar na PDP ya shawarci deleget din cewa kada su aikata wani abin da zai jefa rayuwar yayansu da jikokinsu cikin mawuyancin hali a nan gaba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Tsohon gwamnan Jihar Anambra kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Peter Obi ya bukaci deleget na jam'iyyar su amshi kudi idan yan takara sun basu, rahoton Daily Trust.

Sai dai ya ce kada su yarda kudin da aka ba su ya sauya musu ra'ayin wanda suke niyyar zaba a yayin zaben fidda gwanni na jam'iyyar da ke tafe.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

Ku Amshi Kuɗin Ƴan Takara Amma Ku Yi Zaɓe Da Hikima, Peter Obi
Ku Amshi Kuɗin Ƴan Takara Idan Sun baku Amma Ku Yi Zaɓe Da Hikima, Peter Obi. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Yayin da ya ke magana da deleget din jam'iyyar ta PDP a jiya a Kaduna, Obi ya ce idan aka zabe shi, zai canja Najeriya daga kasa wacce bata kera komai zuwa kasa mai samarwa duniya abin da za su siya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina rokon ku; ku yi kokarin gina wa yayan ku kasa ta gari. idan kun karbi kudin, kada ku bari kudin ya sauya muku ra'ayin wanda za ku zaba. Idan an baku kudi, ku karba," in ji shi.

2023: Tsohuwar Matar Shugaban APC Na Kasa Ta Siya Fom Din Takarar Gwamna a Nasarawa

A wani labarin, Fatima Abdullahi, tsohuwar matar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ta siya fom din takarar gwamnan Jihar Nasarawa, The Sun ta rahoto.

Za ta tsaya takarar ne don a yi zaben fidda gwani na jihar nan da wata daya, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Yayin da ta ke bayani bayan tuntubar shugabannin APC a ofishin jam’iyyar da ke Lafia, ranar Juma’a, Fatima ta ce ta tsaya takarar ne don gyara akan kura-kuran da wannan mulkin ya yi.

A cewarta, Jihar Nasarawa tana bukatar shugaba mai hangen nesa da kuma jajircewa don ciyar da jihar gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel