Watakila Jonathan ya shiga takara a asirce, Jam'iyyar APC ta ce mutum 28 na neman mulki

Watakila Jonathan ya shiga takara a asirce, Jam'iyyar APC ta ce mutum 28 na neman mulki

  • Mutane 28 suka cire N100m domin sayen fam din neman shiga zaben shugaban Najeriya a APC
  • Kakakin jam’iyyar APC mai mulki ya ce mutane uku ne ba su dawo da fam din shiga takaran ba
  • Wannan yana nufin APC ta tashi da Naira biliyan 2.8 daga masu neman zama shugaban kasa a 2023

Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta tabbatar da cewa mutane 28 ta saidawa fam din neman takarar shugaban kasa domin shiga zabe mai zuwa.

Kamar yadda rahoto The Cable na ranar Laraba, 18 ga watan Mayu 2022 ya bayyana, wasu daga cikin wadanda suka saye fam, ba su dawo da shi ba.

Da aka yi hira da Sakataren yada labarai na APC na Najeriya, Felix Morka, ya bayyana cewa mutane uku ba su cike fam dinsu, sun dawo da shi ba.

Kara karanta wannan

‘Dan takaran Shugaban kasa ya ce zai nemawa mutum miliyan 20 aiki ranar da ya karbi mulki

Felix Morka ya ce wadannan mutane su ne gwamnan CBN, Godwin Emefiele, Ministan fetur, Timipre Sylva da Ministan kwadago, Dr. Chris Ngige.

Abin da Felix Morka ya fada

“Mu na da mutane 28 da ke neman takara da sun saye fam. Da mu ka kirga karshe, mun samu mutane 25 da suka dawo da fam dinsu."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Akwai uku da ba su cike fam din na su ba – Sanata Chris Ngige, Godwin Emefiele, da Timipre Sylva." - Felix Morka.

Jonathan
Dr. Goodluck Ebele Jonathan wajen taro a Bayelsa Hoto: jonathangoodluck
Asali: Facebook

Jaridar ta ce Mai magana da yawun bakin APC ya yi watsi da zargin da ake yi na cewa wasu na sayen fam ne kurum domin a tarawa jam’iyya kudin zabe.

A cewar Morka, duk wani mai kudi zai iya fansar fam idan yana ganin ya dace da shugabanci, hakan ta sa jam’iyyar ta yi ciniki sosai da kudin shiga takara.

Kara karanta wannan

Yadda Jam’iyyar APC ta samu tayi wa Yari, Marafa da Gwamna Matawalle sulhu a Zamfara

Morka ya ce APC ba za ta duba cancantar ‘dan takara ba sai an zo tantance masu neman mukamai. Amma a matakin saida fam, kofarsu a bude ta ke.

Takarar Jonathan a APC

Sanannen abu ne wasu sun saye fam da sunan Dr. Goodluck Jonathan, amma tsohon shugaban kasar bai karba ba. Har yau ba a sake jin inda aka kwana ba.

Da kakakin na APC ya ke fadar wadanda ba su dawo da fam dinsu ba, bai ambaci sunan Jonathan ba, hakan ya nuna kila an cike masa fam din, an dawo da shi.

Sakataren yada labaran na APC ya yi gum a kan batun rade-radin takarar Jonathan a zaben 2023.

Kudin kamfe APC ta ke tarawa

Kwanakin baya aka ji labari Sakataren yada labaran PDP na kasa ya fitar da jawabi, yana zargin Gwamnatin APC da taba asusun gwamnati domin a lashe zabe.

Debo Ologunagba ya ce APC ta tsula kudin fam ne saboda ta iya tara kudin da za ta shiga zaben 2023. Jam'iyyar ta samu biliyoyin kudi daga masu sayen fam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng