‘Dan takaran Shugaban kasa ya ce zai nemawa mutum miliyan 20 aiki a ranar da ya karbi mulki

‘Dan takaran Shugaban kasa ya ce zai nemawa mutum miliyan 20 aiki a ranar da ya karbi mulki

  • Mista Tein TS Jack-Rich ya na so ya yi takarar kujerar shugaban Najeriya a jam’iyyar APC a 2023
  • Matashin ya yi alkawari gwamnatinsa za ta yi sanadiyyar da mutane miliyan 20 za su samu aiki
  • A rana daya Tein TS Jack-Rich yake sa ran kawo karshen zaman kashe wandon mutum miliyan 20

Abuja - Mai neman zama shugaban kasa a karkashin APC, Tein TS Jack-Rich ya sake jaddada cewa idan ya samu mulki, ba zai rika karbar aron kudi ba.

Jaridar Leadership ta rahoto Tein TS Jack-Rich yana cewa gwamnatinsa ba za ta ci bashin ko sisi ba, sannan zai samarwa matasan kasar nan hanyar cin abinci.

Da ‘yan jarida su ka yi hira da shi a karshen makon jiya, ‘dan siyasar ya yi alkawarin cewa a ranar farko da ya yi a ofis, zai nemawa mutane fiye da miliyan 20 aiki.

Kara karanta wannan

Dan takarar APC Tinubu: Ba zan sarara ba a siyasa har sai na mulki Najeriya

Matashin zai kawo hanyar da mutane za su samu abin yi domin a rage zaman kashe wando ne ta hanyar gyara harkar gas da danyen mai da Najeriya ke da su.

Har ila yau, Jack-Rich ya ce har ya sauka daga kujerar shugaban kasa, ba zai ci wa Najeriya bashi ba. A halin yanzu ana kukan gwamnati ta na yawan cin bashi.

Ayyuka 26, 000 a kowace LGA

“Mulkina zai sa mu fi cin moriyar arzikin da mu ke da shi. Zan samar da ayyuka 26, 000 a kowace karamar hukumar Najeriya a ranar farko da na shiga ofis.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Zan cin ma wannan buri. Idan na kirkiri ayyuka na kai-tsaye 26, 000 a ranar farko a ofis a kananan hukumomi 774, a shekara daya za a kawar da talauci.”

Tein TS Jack-Rich

‘Dan takaran APC
Tein Jack-Rich mai takara a APC Hoto: thisnigeria.com
Asali: UGC

Wani irin shugaba ake bukata?

Kara karanta wannan

‘Dan shekara 47 mai ji da kudi ya saye fam din APC, zai yi takarar Shugaban kasa a 2023

Business Day ta rahoto Jack-Rich yana cewa ana bukatar shugaban kasar da zai iya habaka tattalin arziki. A halin yanzu ana kuka da tattalin arzikin kasar.

Hamshakin ‘dan kasuwar ya ce akwai bukatar a kawo abubuwan more rayuwan da za su taimaka wajen bunkasa fasahar zamani, ta haka jama'a za su samu aikin yi.

Baya ga sanin tattali, Jack-Rich ya ce Najeriya ta na bukatar shugaban kasar da za a girmama a duk fadin Duniya, wanda zai iya zama da masu zuba hannun jari.

A cewarsa, wanda zai karbi mulki yana bukatar ya iya ganin kowane yankin Najeriya ya amfana da arzikin danyen man fetur da ake da shi a bangaren Neja-Delta.

Jack-Rich ya ayyana niyyar takara

Ana da labari Tein Jack-Rich ya shiga takara, ya na harin kujerar Muhammadu Buhari. Rich ya nada Malam Isa Yuguda ya zama shugaban yakin neman zabensa.

Tunihar Mista Jack-Rich ya saye fam din neman zama ‘dan takarar shugaban Najeriya a APC a kan N100m, har ya cike fam din, yana jiran ranar zaben tsaida gwani.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Asali: Legit.ng

Online view pixel