Ganduje Da Barau Sun Bi Murtala Garo Har Gida Don Ƙoƙarin Hana Shi Ficewa Daga APC

Ganduje Da Barau Sun Bi Murtala Garo Har Gida Don Ƙoƙarin Hana Shi Ficewa Daga APC

  • Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano da Sanata Barau Jibrin sun ziyarci Murtala Garo a gidansa bayan 12 na daren Laraba don kokarin hana shi fita daga APC
  • Rahotanni sun bayyana cewa Garo bai ji dadin yadda Ganduje ya janye takarar sanata ya bar wa Jibrin Barau ba duba da cewa ba su ga maciji
  • Majiyoyi sun kuma rahoto cewa Garo baya jin dadin yadda Ganduje ke tafiyar da al'amurrar jam'iyya ta yadda mutane da dama ke fita hakan yasa shima ya ke duba yiwuwar komawa PDP ya yi wa Atiku aiki

Jihar Kano - Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje da sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Barau Jibrin sun ziyarci dan takarar mataimakin gwamna na sassanci a APC, Murtala Garo, bayan karfe 12 na daren Alhamis.

Kara karanta wannan

Shekarau: Abin Da Ya Sa Na Fita Daga APC Na Koma NNPP Don Haɗuwa Da Kwankwaso

Daily Nigerian ta tattaro cewa gwamnan, a wata fita da ya yi ba tare da cikakken tawagarsa ba, ya ziyarci gidan Garo da ke Railway Quaters don rokonsa kada ya fita daga APC.

Kano: Ganduje Da Barau Sun Bi Murtala Garo Har Gida Don Ƙoƙarin Hana Shi Ficewa Daga APC
Ganduje Da Barau Sun Bi Murtala Garo Har Gida Don Ƙoƙarin Hana Shi Fita Daga APC. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata majiya wacce ke da masaniya kan lamarin ta ce Ganduje ne ya fara isa gidan kafin daga bisani Jibrin ya iso ya tarar da shi.

Majiyar ta kara da cewa mutanen uku suna ganawar sirri a halin yanzu, rahoton Daily Nigerian.

Dalilan da suka sa Garo ke duba yiwuwar fita daga APC

A baya-bayan nan Garo ya nuna damuwarsa kan janyewa daga takarar Sanata da Ganduje ya yi don bawa Jibrin dama, wanda shi kuma abokin adawarsa ne na siyasa.

Don nuna rashin amincewarsa, da kuma rashin jin dadin yadda gwamnan ya gaza dakatar da yadda mutane da dama ke fita daga APC, Garo ya ki halartar taruka a gidan gwamnati da wajenta, ya bar Nasir Gawuna shi kadai.

Kara karanta wannan

Sai dai a buga, Sanata mai-ci ya ce ba zai janyewa Gwamna takarar Majalisa a APC ba

Majiyoyi sun bayyana cewa akwai yiwuwar tsohon kwamishinan na kananan hukumomi zai koma jam'iyyar PDP domin yi wa surukinsa, Atiku Abubakar aiki a takararsa na shugaban kasa.

Jam'iyyar ta APC a Kano ta shiga wani hali, yayin da mambobinta da dama suke fita suna koma wa wasu jam'iyyun a baya-bayan nan.

Mataimakin Kakakin Majalisar Kano Ya Fice Daga APC, Ya Bi Kwankwaso Jam'iyyar NNPP

A wani rahoton, mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Zubairu Hamza Massu, ya fice daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC ya koma New Nigeria People's Party, NNPP, rahoton Daily Nigerian.

Mr Massu, ɗan siyasa daga mazabar Kano ta Kudu, ya sanar da ficewarsa daga APC cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar na APC a mazabar Massu.

Ɗan majalisar ya bayyana rikice-rikicen jam'iyyar da rashin demokradiyya ta cikin gida a matsayin dalilin ficewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel