Shekarau: Abin Da Ya Sa Na Fita Daga APC Na Koma NNPP Don Haɗuwa Da Kwankwaso

Shekarau: Abin Da Ya Sa Na Fita Daga APC Na Koma NNPP Don Haɗuwa Da Kwankwaso

  • Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan Jihar Kano ya bayyana dalilan da ya sa ya bar jam’iyyar APC ya koma NNPP
  • Sanatan mai wakiltar Kano ta tsakiya ya bayyana jerin dalilan ne yayin da Channels TV ta tattauna da shi a ranar Laraba
  • A cewarsa, ya sauya shekar ne bayan jam’iyyar APC ta gaza samar da masalaha tsakanin bangarensa da na Ganduje

Jihar Kano - Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a yanzu haka, Ibrahim Shekarau ya bayyana dalilinsa na barin jam’iyya mai mulki, APC inda ya koma NNPP.

Ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da Channels TV ta yi da shi a ranar Laraba kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya bi Shekarau har gida, ya ba shi takarar Sanatan da ta canza lissafin 2023

Shekarau: Abin Da Ya Sa Na Fita Daga APC Na Koma NNPP Don Haɗuwa Da Kwankwaso
Shekarau: Dalilin Da Ya Sa Na Fita Daga APC Na Koma NNPP Don Haɗuwa Da Kwankwaso. Hoto: Ibrahim Shekarau.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu rahotanni akan yadda tsohon gwamnan ya koma NNPP bayan watanni kadan da su ka dinga samun matsalar shugabanci da Abdullahi Ganduje, gwamnan Jihar Kano.

Sauya shekar tasa ta na nufin cewa ya koma bayan bangaren Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan Jihar Kano, na NNPP.

Ya ce Mai Mala Buni bai yi kokarin hada kan bangarorin jam’iyyar ba

Yayin bayani akan dalilinsa na sauya shekar, Shekarau ya ce APC ta kasa samar da masalaha tsakanin bangarensa da na Ganduje, hakan ya sa ya sauya shekar.

The Cable ta ruwaito inda ya ci gaba da cewa:

“Gaskiya ne wannan. Sakamakon wasu abubuwa da su ka wakana a makwannin baya ko kuma watannin baya, sannan kuma na tuntubi mutane daga mazabun da na ke wakilta shiyasa na bar jam’iyyar.
“Sai dai maimakon shugaban jam’iyyar na lokacin, Mai Mala Buni, ya hada taro don samar da masalaha akan matsalar cikin gida bayan sa’o’i kadan kafin kotun daukaka kara ta kammala shari’ar, sai su ka yi gaggawar bayar da takarda ga dayan bangaren.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Shekarau ya karbi katinsa na zama cikakken dan jam’iyyar NNPP

“Mun yi gaggawar wucewa kotun koli, inda ta tsaya akan hukuncin da kotun daukaka kara ta yi akan cewa matsalar ta cikin jam’iyya ce don haka kamata ya yi jam’iyyar ta samar da masalaha tsakanin bangarorin guda biyu.”

Ya ci gaba da bayyana yadda su ka dinga zama da shugabancin jam’iyyar, karkashin Mai Mala Buni kowa ya na neman mafita amma abin ya ci tura.

A cewarsa duk rahotannin da aka dinga saki a kafafen sada zumunta ba na gaskiya ba ne. Kotun koli ba ta ce ta aminta da shugabancin bangaren Abdullahi Abass ba. Ba haka hukuncin ya ke ba.

Ya ce ya yi iyakar kokarinsa amma gwamnan jihar ne ya dinga dakatar da shi

Ya shaida yadda bayan sababbin shugabannin jam’iyyar sun zo, hankali ya koma kan shirye-shiryen yin zaben fidda gwani.

A cewarsa:

“Na yi iyakar kokarina wurin ganin na kawo hadin kai tsakanin bangarorin guda biyu don a zauna a tattauna. Amma a ko wanne lokaci gwamnan ya na nuna min iyakata. Alamu sun nuna cewa ba ya bukatar hadin kan bangarorin.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel