Sai dai a buga, Sanata mai-ci ya ce ba zai janyewa Gwamna takarar Majalisa a APC ba

Sai dai a buga, Sanata mai-ci ya ce ba zai janyewa Gwamna takarar Majalisa a APC ba

  • Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya ce bai hakura da neman takarar kujerar da yake kai a zaben 2023 ba
  • Sabi Abdullahi shi ne Sanata mai wakiltar yankin Arewacin jihar Neja tun 2015 a jam’iyyar APC
  • Duk da Gwamna Abubakar Sani Bello yana neman kujerarsa, 'Dan majalisar ya ce ba zai janye masa ba

Niger - Mataimakin shugaban mai tsawatarwa a majalisar dattawan Najeriya, Aliyu Sabi Abdullahi, ya musanya rade-radin cewa ya hakura da takara.

Aliyu Sabi Abdullahi ya ce yana nan a kan bakarsa na sake neman kujerar Sanatan Arewacin jihar Neja, duk da Gwamna Abubakar Sani Bello ya na takara.

Daily Trust ta rahoto cewa Aliyu Sabi Abdullahi ya bayyana haka ne a lokacin da ya zanta da ‘ya ‘yan jam’iyya da magoya bayansa a New Bussa, a garin Borgu.

Kara karanta wannan

2023: Saura kwana 10 zabe, an shiga yamutsi a PDP game da wanda za a tsaida takara

Sanata Aliyu Sabi Abdullahi yake cewa masu yada labarin fasa takararsa a zaben 2023, ba kowa ba ne face wadanda suke tsoron farin jini da karfinsa a siyasa.

Ina nan kan batun takara - Sabi

‘Dan majalisar ya ce zuwansa New Bussa ya kara tabbatarwa magoya bayansa cewa bai janye ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ya ku maza da mata masu daraja, zuwa na gabanku a nan zai tabbatar maku da cewa har yanzu ina takara.”

Gwamnan Neja
Gwamna Abubakar Sani Bello Hoto: @GovNiger
Asali: Twitter

“Ina neman Sanatan yankin Arewacin jihar Neja. Ban janye takarata ba, kuma ba ni da niyyar janye takarar.”

Ba zai ci amanar masoyansa ba

Jaridar ta rahoto tsohon mai magana da yawun bakin majalisar dattawan ya na cewa cin amanar mutanensa ne ya ja da baya tun da masoya sun saya masa fam.

A halin yanzu Mai girma Abubakar Sani Bello wanda ya fito daga yankin Kontagora yana harin wakiltar mutanen Neja ta Arewa a majalisar dattawa a APC.

Kara karanta wannan

Dan takarar APC Tinubu: Ba zan sarara ba a siyasa har sai na mulki Najeriya

Jikantoro ya fifita takarar Gwamna

Independent ta ce kwanan nan aka ji shugaban APC na jihar Neja, Alhaji Haliru Jikantoro, yana cewa su na goyon bayan takarar Alhaji Abubarkar Sani Bello.

Haliru Jikantoro ya ce Sani Bello ne kadai ‘dan takarar da suka sani a mazabar Arewacin Neja. Hakan ta sa wasu ke zargin shugaban na APC da yin son kai.

Sanata Enang zai nemi Gwamna

Ku na da labari cewa Ita Enang ya rubuta takardar murabus da ta tabbatar da ya ajiye aikinsa a fadar shugaban Najeriya domin ya nemi gwamnan Akwa Ibom.

Sanata Enang ya godewa Muhammadu Buhari da ya yi aiki da shi na shekaru kusan 7 a matsayin mai bada shawara a arkokin majalisa da na harkar Neja Delta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel