Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje

Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje

  • Siyasar Kano ta ƙara rikicewa musamman tsakanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau
  • Bayan ziyarar Ganduje gidan Shekarau don hana shi komawa NNPP, Kwankwaso ya tura tawaga kafin zuwansa gidan Shekarau
  • Fadar shugaban ƙasa ta yi kokarin shiga tsakani, ta tura jirgi Kano ya ɗakko gwamna Ganduje da Sanata Shekarau

Kano - Awanni ƙalilan bayan gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya kai ziyara gidan Sanata Ibrahim Shekarau, domin hana shi komawa NNPP, Jagora Rabiu Musa Kwankwaso ya tura tawagar wakilai.

Kwankwaso, wanda ke shirin karɓan Shekarau zuwa NNPP ranar Asabar, ya samu labarin motsin Ganduje, nan take ya kira gidan Shekarau inda ya sanar musu yana nan tafe.

Tawagar jam'iyyar NNPP.
Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje Hoto: Ahmad Lawan Garba/fb
Asali: Facebook

Duk da dai babu cikakken bayani kan abinda suka maida hankali, amma wata majiya tace zuwan ba zai rasa nasaba da tabbatar wa idan Shekarau na kan bakarsa na komawa NNPP.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Shekarau Ya Ƙi Bin Ganduje Zuwa Ganin Buhari a Abuja Bayan Gano Maƙarƙashiyar Da Aka Shirya Masa

Sakataren jam'iyyar NNPP a Kano, Hamisu Sadi Ali, ya tabbatar da kai ziyara gidan Shekarau a shafinsa na dandalin Facebook.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakataren yace:

"Yanzun nan bayan tattaunawa mai muhimmanci da Malam Ibrahim Shekarau a gidansa da ke Munduɓawa, Bompai cikin birnin Kano."

Daga cikin tawagar da suka shiga ganawa da tsohon gwamnan jim kaɗan bayan tafiyar Ganduje akwai Sakataren NNPP, Hamisu Sadi Sidi, Sakataren tsare-tsare, Dakta Kabiru Usaini da kakakin jam'iyya, Abdulahi Rogo.

Fadar shugaban ƙasa ta tsoma baki kan rikicin APC a Kano

A wasu rahotanni ta bayan fage, an gano cewa bayan ziyarar da Ganduje ya kai gidan Shekarau, fadar shugaban ƙasa ta yi shawarin shiga tsakani don sulhunta su.

Fadar shugaban ƙasa ta tashi jirgi zuwa Kano ya ɗakko manyan jiga-jigan biyu zuwa Abuja domin maslaha ta ƙarshe a tsakanin su.

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban Ma'aikatan Fadar Ganduje, Shugaban Karamar Hukuma, Ƴan Majalisa 2, Auditan APC Da Shugaban Matasa Duk Sun Koma NNPP

Wata majiya ta bayyana cewa ana tsammanin Ganduje da Shakarau za su shilla Abuja a daren domin halartar taron a Abuja.

A wani labarin kuma Kallo ya koma sama yayin da Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigan APC sun dira filin Malam Aminu Kano

Kallo ya koma sama baki ya ƙi rufuwa yayin da Sanata Kwankwaso ya dira Kano daga Abuja tare da jiga-jigan APC mai mulki.

Tsohon hadimin Buhari, Kawu Sumaila, Albdulmumini Jibrin, suna cikin tawagar da ta dira Filin Malam Aminu Kano tare da Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Online view pixel