Ganduje ya kira zaman gaggawa a sakamakon rikicin da ke neman kunnowa APC a Kano

Ganduje ya kira zaman gaggawa a sakamakon rikicin da ke neman kunnowa APC a Kano

  • Har yanzu babu jituwa a APC na reshen jihar Kano duk da zaman sulhun da aka yi a makon jiya
  • Da alama Murtala Sule Garo bai ji dadin sasantawar da Gwamna ya yi da Sanata Barau Jibrin ba
  • Ana cigaba da samun rikici tsakanin kusoshin jam’iyyar APC na bangaren Arewacin jihar Kano

Kano - Rahoton da ya fito daga Sahelian Times ya nuna cewa har yanzu ba a kawo karshen rikicin gidan da ya addabi jam’iyyar APC a jihar Kano ba.

A halin yanzu an samu sabani a dalilin goyon bayan da Barau Ibrahim Jibrin ya samu na neman takarar Sanatan Arewacin Kano a karkashin APC a 2023.

Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sasanta da ‘yan bangaren Barau Ibrahim Jibrin, ta hanyar janye takarar Sanata da ya yi niyyar yi a APC.

Kara karanta wannan

Yadda Jam’iyyar APC ta samu tayi wa Yari, Marafa da Gwamna Matawalle sulhu a Zamfara

Wannan mataki da Gwamnan ya dauka bai yi wa Alhaji Murtala Sule Garo da mutanensa dadi ba.

Garo v Maliya

Garo shi ne ya sauka daga kujerar Kwamishinan harkokin kananan hukumomi, kuma wanda aka ayyana a matsayin ‘dan takarar mataimakin gwamnan Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun ba yau ba, ana ta samu rigingimu tsakanin Murtala Garo da Sanatan yankin Kwamishinan watau Arewacin Kano, Barau Jibrin duk da cewa duk ana APC.

Ganduje
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje Hoto: @aaibrhim1
Asali: Facebook

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa Murtala Garo bai ji dadin sulhun da Mai girma Abdullahi Umar Ganduje ya yi da jagoran na tafiyar kungiyar ta G7 ba.

An yi cacar baki da 'Dan Sarki

A dalilin haka ne aka ji tsohon Kwamishinan ya yi musayar kalamai da shugaban jam’iyyar APC na reshen jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas a ranar Litinin.

Kamar yadda mu ka ji labari, Garo ya yi wa Gwamna rashin kunya a daren yau da suka hadu.

Kara karanta wannan

Manyan mutanen da suka taimakawa Janar Sani Abacha ya saci Dala miliyan 23 a kasar waje

Da Alhaji Abdullahi Abbas ya nemi ya jawo hankalinsa, sai rigima ta kaure tsakaninsu biyu. A baya dai ana ganin jirgi daya ya dauko Abbas da Garo a jam'iyya.

Ganin yadda abin ke nema ya dauki wani salo, Gwamna Ganduje ya kira taron gaggawa na masu ruwa da tsaki da karfe 3:00 na yau domin a dinke wannan baraka.

Ganduje ya ci girma

A makon nan mu ka kawo maku rahoto cewa Mai girma gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya hakura da neman kujerar Sanata a zabe mai zuwa.

Gwamnan ya dauki wannan matsaya ne bayan sasantawa da aka yi tsakanin bangarensa a APC da kuma tsagin Sanata Barau Ibrahim Jibrin da k tare da 'yan taware.

Asali: Legit.ng

Online view pixel