Yajin aikin ASUU: Daliban jami'a sun fusata, sun ba lakcarori da gwamnati wa'adi su bude jami'o'i

Yajin aikin ASUU: Daliban jami'a sun fusata, sun ba lakcarori da gwamnati wa'adi su bude jami'o'i

  • Kungiyar daliban Najeriya sun fusata, sun bayyana matakin da za su dauka idan ba a janye yajin aiki ba
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jami'o'in Najeriya ke ci gaba da zama a kulle saboda yajin aikin kungiyar malamai ta ASUU
  • ASUU a makon nan ta kara wa'adin yajin aikinta zuwa wani lokaci saboda kin sauararanta da gwamnatin najeriya ta yi

Jihar Legas - Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) reshen kudu maso gabas ta baiwa gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) wa’adin kwanaki tara su bude dukkan jami’o’in gwamnati.

Ko’odinetan shiyyar NANS ta Kudu maso Gabas, Mista Moses Onyia, ya ba da wa’adin ne a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Lillian Orji, ya fitar a madadinsa, a ranar Talata a Enugu.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Yadda dalibai ke neman mafita ga yajin aikin ASUU
Yajin aikin ASUU: Daliban jami'a sun fusata, sun ba malamansu wa'adin bude jami'o'i | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

ASUU, a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, ta tsawaita yajin aikin gargadi na watanni uku da karin wasu watanni ukun, wanda ta shiga tun a ranar 14 ga Fabrairu, 2022, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Matakin ASUU dai shi ne don matsawa gwamnati wajen biyan bukatunta da suka hada da farfado da jami'o'in gwamnati, samun alawus-alawus na ilimi da dai sauransu.

Sanarwar ta ce ya kamata gwamnati da ASUU su yi abin da ya kamata kafin kwanaki tara. Ta kara da cewa rashin yin hakan a cikin ko kuma a karshen wa’adin zai kai ga dalibai su dauki mataki mai tsauri.

Ya ce da tsawaita yajin aikin na ASUU na karin watanni uku wanda zai sa ya zama jimillar watanni shida, za a tilasta wa daliban manyan makarantun Najeriya zama a gida ba tare da hazaka ba.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Sanarwar ta kuma kara da cewa, hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘ya’yan mafi yawan ‘yan siyasa da manyan jami’an gwamnati ke shiga manyan jami’o’i a kasashen ketare suna samun karatu ba tare da tsangwama ba.

Sanarwar ta ce:

“Ba za mu kara yin shuru ba ko kuma mu yi biris da cewa komai yana tafiya daidai domin ba mu da kwanciyar hankali.
“Ba tare da wata shakka ba kuma a tare, mun ce a’a da babbar murya ga wannan tsawaita yaji, kuma bisa ga wannan sanarwar da muka fitar mun sanar da gwamnati, ASUU, hukumomin tsaro da kuma talakawa matsayinmu”.

Ku share ASUU ku koma aji: Shawarin gwamnan APC ga lakcarorin da ke yajin aiki

A wani labarin, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi kira ga kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta jami’ar jihar Yobe da su sake duba matsayar su kan yajin aikin da kungiyar ta kasa ke ci gaba da yi.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Buhari Ya Roƙi ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ya Ba Wa Ɗalibai Haƙuri

Buni, wanda ya gana da mahukuntan makarantar da kungiyar, ya ce gwamnatin jihar da jami’ar ba su da wata matsala a tsakaninsu, don haka babu hujjar rufe jami'ar, inji rahoton Premium Times.

Malaman jami'o'i sun shafe fiye da watanni biyu suna yajin aiki saboda neman ingantacciyar walwala da kayan aiki don habaka sana'arsu ta koyarwa.

Gwamnan wanda sakataren gwamnatin jihar Baba Malam Wali ya wakilta a wurin taron, ya kuma yi kira ga malaman da su yi la’akari da halin da daliban da yajin aikin ya shafe ke ciki, inji rahoton Daily Post.

Dalibai sun shiga tasku, ASUU ta tsawaita yajin aikinta da karin watanni 3

A wani labarin, kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta tsawaita yajin aikin da take yi da makwanni goma sha biyu, kamar yadda shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana a ranar Litinin, inji majiyar gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Malaman makarantun Poly sun bi sahu, ASUP ta sanar da shiga yajin aiki

Wannan na zuwa ne bayan da dalibai da iyayensu ke ci gaba da jiran karshen yajin aikin da ya barke a shekarar nan.

A wata sanarwa da ya fitar bayan taron malaman jama'o'i da aka gudanar a Jami’ar Abuja, shugaban ASUU ya ce sun yanke shawarar baiwa gwamnati isasshen lokaci domin warware duk wasu matsaloli da malaman ke fuskanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel