Hadiza Sabuwa Balarabe, wasu mata 3 da ke rike da matsayin Mataimakan Gwamna a yau

Hadiza Sabuwa Balarabe, wasu mata 3 da ke rike da matsayin Mataimakan Gwamna a yau

  • Duk da an dade ana siyasa a Najeriya, sai dai ba a saba ganin mata sun rike manyan mukamai ba
  • Maza ne suka fi yawa a majalisun dokoki da na tarayya, haka zalika su ne suka cika majalisar FEC
  • Amma akwai wasu matan da suka yi zarra a cikin takwarorinsu, suka zama na biyu a jihohinsu

Legit.ng Hausa ta zagaya jihohin kasar nan 36, ta tattaro jihohin da mace ta ke rike da mukami na biyu mafi girma watau mataimakiyar gwamna a jihar.

Akwai mace daya a yankin Arewacin Najeriya da ke rike da wannan kujerar, ragowar mataimakan gwamnonin da ake da su, su na yankin kudu.

A babban birnin tarayya watau Abuja inda ake da Minista a maimakon gwamna, karamar Ministar da ke mulki a yanzu, Ramatu Tijjani Aliyu, mace ce.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Jihohin da mata ne #2:

1. Ribas

A jihar Ribas, Dr. Ipalibo Harry-Banigo ke rike da kujerar mataimakiyar gwamna tun 2015. A 1995 ta zama sakatariyar gwamnatin jihar Ribas tana shekara 42.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kafin shigar ta siyasa ta rike Darekta a ma’aikatar lafiya, Kwamishinar rikon kwarya, Darekta Janar, Sakataren din-din-din da shugaban ma’aikatan gwamnati.

Yanzu haka Harry-Banigo za ta yi takarar Sanatar Ribas ta yamma a karkashin jam’iyyar PDP.

Hadiza Sabuwa Balarabe
Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe a bakin aiki Hoto:@ depgovkaduna
Asali: Facebook

2. Enugu

Mai girma Cecilia Ezeilo ita ce mataimakiyar gwamna a jihar Enugu. Tun a zaben 2015, Ifeanyi Ugwuanyi ya dauko ta a matsayin wanda za su yi takara tare a PDP.

Hon. Cecilia Ezeilo ta shiga siyasa ne a 2011, ta wakilci mutanen Ezeagu a majalisar dokokin Enugu. Tun 1991, ba a samu macen da ta rike wannan kujera a jihar ba.

Hon. Ezeilo ta fito ne daga kauyen Amoke a yankin Udi inda ta ke shirin wakilta a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

3. Kaduna

Ita ma Hadiza Sabuwa Balarabe wanda ta zama mataimakiyar gwamnar jihar Kaduna bayan zaben 2019 kwararriyar likita ce. Ita ce ta maye gurbin Marigayi Bala Bentex.

An haifi Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe ne a karamar hukumar Sanga da ke kudancin jihar Kaduna. Ta fara karatunta a Soba, har ta samu zuwa jami’ar UNIMAID a 1980s.

A baya an yi tunanin Balarabe za ta nemi kujerar gwamnan Kaduna a APC, amma ba ta tabbata ba.

Kalu ya fasa takarar Shugaban kasa

Orji Uzor Kalu wanda yana cikin masu neman zama Shugaban kasa a APC ya hakura da maganar. An ji labari ya bayyana matsayin da ya dauka tun ba zai nemi tikiti ba.

Sanata Kalu ya ce zai goyi bayan Sanata Ahmad Lawan a zaben fitar da gwani da za ayi. Dalilin goyon bayan shugaban majalisar shi ne ya fito daga Arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Asali: Legit.ng

Online view pixel