Ahmed Yerima: Kiristoci Sun Mori Dokar Shari'ar Musulunci Da Na Kafa a Lokacin Da Na Ke Gwamna a Zamfara

Ahmed Yerima: Kiristoci Sun Mori Dokar Shari'ar Musulunci Da Na Kafa a Lokacin Da Na Ke Gwamna a Zamfara

  • Ahmed Yerima, tsohon gwamnan Jihar Zamfara, ya ce kiristocin jiharsa sun amfana daga dokar shari’ar musuluncin da ya kafa lokacin ya na kan karagar mulki
  • A ranar Talata Yerima ya bayyana hakan yayin da Channels TV ta tattauna da shi a karkashin shirinta na ‘Siyasa a Yau’
  • A cewarsa, a shekarar 1999 ne ya gabatar da shari’ar musulunci a jihar, daga nan sauran jihohin arewa su ka bi sahun shi

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Ahmed Yerima ya ce Kiristocin jiharsa sun amfana kwarai daga dokar musuluncin da ya kafa a jiharsa lokacin ya na gwamna, The Cable ta ruwaito.

A ranar Talata ya bayyana hakan yayin da Channels Television ta zanta da shi a shirinta na ‘Politics Today’.

Ahmed Yerima: Kiristoci Sun Mori Dokar Shari'ar Musulunci Da Na Kafa a Lokacin Da Na Ke Gwamna a Zamfara
Ahmed Yerima: Kiristocin Zamfara sun amfana daga dokar shari’ar musuluncin da na kafa lokacin ina gwamna. Hoto: The Cable.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Tsohon gwamnan ya ce tun watan Oktoban 1999 ya kafa dokar wacce daga nan sauran jihohin arewa su ka bi sahunsa.

Yayin da aka tambayeshi idan ya na tunanin arewa ta fi zaman lafiya lokacin da dokar musuluncin, gwamnan cewa ya yi, “kwarai kuwa, a lokacinsa”.

Yerima ya ce lokacin yana gwamna babu ta’addanci a Jihar Zamfara

Ya ci gaba da cewa:

“A lokacin yana gwamna, shugaban kasa Obasanjo ya bayyana cewa Jihar Zamfara ba ta fama da ta’addanci gaba daya. Sun ce kason ta’addanci a jihar zamfara 0.2 bisa dari ne.
“Shari’a tana nufin adalci da daidaito. Ku tambayi kiristocin Jihar Zamfara, za su fada muku cewa a lokacin sun ji dadi.
“Kwanan nan da na bayyana kudirina na takara a Abuja, shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN reshen Jihar Zamfara yana wurin. Ya sanar da ‘yan Najeriya irin amfanin da kiristoci su ka samu karkashin mulkina. An samu adalci da ci gaba kwarai.”

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

Ya ce bai taba tilasta wa wani kirista bin dokar musuluncin ba

A wata tattaunawa da manema labarai su ka yi da Yerima, ya ce ya gabatar da dokar shari’ar musulunci a Zamfara ne wacce ta yi daidai da kundin tsarin mulki wanda ya ba kowa damar yin addininsa.

A batun yadda ake masa kallon mai tsawwalawa a addini, Yerima ya ce zai yi yaki da jahilci kuma ya tabbatar duk abinda zai yi ya dace da kundin tsarin mulki.

Ya kara da cewa:

“Ban taba tilasta wa wani Kirista bin dokar musulunci ba saboda ba haka kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar ba.”

2023: Tsohuwar Matar Shugaban APC Na Kasa Ta Siya Fom Din Takarar Gwamna a Nasarawa

Fatima Abdullahi, tsohuwar matar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ta siya fom din takarar gwamnan Jihar Nasarawa, The Sun ta rahoto.

Za ta tsaya takarar ne don a yi zaben fidda gwani na jihar nan da wata daya, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dubunnan ‘Ya ‘yan APC sun yi watsi da Jam’iyya mai mulki zuwa NNPP a jihar Zamfara

Yayin da ta ke bayani bayan tuntubar shugabannin APC a ofishin jam’iyyar da ke Lafia, ranar Juma’a, Fatima ta ce ta tsaya takarar ne don gyara akan kura-kuran da wannan mulkin ya yi.

A cewarta, Jihar Nasarawa tana bukatar shugaba mai hangen nesa da kuma jajircewa don ciyar da jihar gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel