Manyan shawarwari 5 da aka yanke yayin da shugabannin APC a kudu maso yamma suka gana da su Tinubu

Manyan shawarwari 5 da aka yanke yayin da shugabannin APC a kudu maso yamma suka gana da su Tinubu

A ranar Juma’a, 6 ga watan Mayu ne, shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a kudu maso yamma suka gana da yan takarar shugaban kasa daga yankin a jihar Lagas.

Tsohon gwamnan jihar Ogun, Cif Olusegun Osoba da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Cif Bisi Akande, ne suka jagoranci taron a Lagos Flag House, Marina, jihar Lagas.\

Manyan shawarwari 5 da aka yanke yayin da shugabannin APC a kudu maso yamma suka gana da su Tinubu
Manyan shawarwari 5 da aka yanke yayin da shugabannin APC a kudu maso yamma suka gana da su Tinubu Hoto: nubu Support Group -TSG
Asali: Facebook

Wadanda suka halarci taron sun hada da:

  • Jigon jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
  • Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo
  • Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi
  • Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola
  • Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila
  • Cif Niyi Adebayo
  • Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo
  • Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun
  • Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola
  • Sakataren jam’iyyar APC na kasa Otunba Iyiola Omisore
  • Sanata Ibikunle Amosun
  • Otunba Gbenga Daniel

Kara karanta wannan

‘Yan siyasan Arewa 10 baya ga Atiku, Kwankwaso, da Yarima masu harin zama Shugaban kasa

Legit.ng ta tattaro cewa an gudanar da taron ne domin tabbatar da ganin cewa an kare ra’ayin kudu maso yamma a zaben fidda gwanin jam’iyyar na shugaban kasa mai zuwa.

Ga wasu daga cikin manyan shawarwari da aka yanke a taron:

1. Shugaban kasa dan kudu maso yamma a 2023

Sabanin kiraye-kiraye da ake yi kan kudu maso gabas ta samar da magajin shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugabannin APC a kudu maso yamma sun yanke shawarar cewa yankin Yarbawa ne zai samar da shugaban kasa na gaba a 2023.

Daya daga cikin wadanda suka shirya taron, Cif Akande ya ce, "Mun hada kai ne don kudu maso yamma ta samar da shugaban kasa a 2023."

2. Babu dan takarar maslaha, dukkanin yan takara na da damar shiga tseren

Kara karanta wannan

2023: Ministan Man Fetur da wani gwamnan APC sun karɓi Fom, sun shiga takarar shugaban ƙasa

Kafin taron, ana ta hasashen cewa an kira taron ne a kokarin ganin kudu maso yamma ya samar da dan takara na maslaha yayin da sauran za su janye.

Sai dai kuma, babu abu makamancin haka da ya faru a taron, majiyoyi sun sanar da Legit.ng. shugabannin APC sun tabbatar da cewar dukkanin yan takara na da damar yin takara.

“Batun wasu su janyewa wani ko dan takarar maslaha baya cikin ajandar” in ji wata majiya.

3. Tinubu vs Osinbajo, Fayemi da sauransu; babu butulci

Shugabannin na APC sun kuma kawo karshen batun butulci.

“An ajiye zancen butulci a gefe yayin da dattawan suka tabbatar da cewar duk wanda ke da muradin yin takarar kowace kujera bai da shinge ta koina,” cewar wata majiya a taron.

4. A gudanar da yakin neman zabe mai tsafta

A wajen taron, shugabannin na APC sun bukaci dukkanin yan takara da su guje ma kalaman raba kan jama’a a yakin neman zabensu.

Kara karanta wannan

2023: Fasto Tunde Bakare ya ayyana neman takarar kujerar Buhari a hukumance

Sun yanke cewa yan takara da magoya bayansu su guji kiran sunaye ko caccaka ta son rai a yakin neman zabensu.

5. Abun da za a yi bayan zaben fidda gwani

Shugabannin na APC sun shawarci yan takara da su ci gaba da hada kansu gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasar.

Sun kuma bukace su da su kasance a bayan duk wanda ya zama dan takarar jam’iyyar, suna masu cewa ya zama dole a mutunta hadin kan kudu maso yamma.

Shugaban kasa a 2023: Aminu Tambuwal ya nuna karfin gwiwar mallakar tikitin PDP

A wani labarin kuma, yayin da yan siyasa ke gwagwarmayar mallakar tikitin takarar shugaban kasa a karkashin inuwar People’s Democratic Party (PDP), Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya nuna karfin gwiwar yin nasara a zaben fidda gwanin jam'iyyar mai zuwa.

Tambuwal ya bayar da tabbacin ne jim kadan bayan ya kada kuri’arsa a taron jam’iyyar PDP na shiyyar arewa maso yamma a wanda aka yi a jihar Kaduna, a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jerin yan takarar shugaban kasa na APC 20 da suka siya fom din N100m, jam’iyyar mai mulki ta tara N1.95bn

Ya ce gudanar da taron jam’iyyar na yankin da aka yi cikin nasara alama ce da ke nuna cewa taronta na kasa zai gudana cikin lumana da nasara a bangarensa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng