Jerin yan takarar shugaban kasa na APC 20 da suka siya fom din N100m, jam’iyyar mai mulki ta tara N1.95bn
Ana tururuwan siyan fom din takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) duk da tsawwala farashinsa da aka yi wanda ya kai naira miliyan 100.
Jam’iyyar mai mulki dai ta tsawaita wa’adin siyar da fom dinta yayin da kasuwa ke kara bude mata.
Zuwa yanzu, akalla yan takara 20 ne suka siya fom din. Yayin da yan takara 19 suka biya naira miliyan 100 kowannensu, mace daya a cikinsu, Uju Kennedy, ce ta biya 50% daidai da tsarin jam’iyyar.
Da wannan, APC ta tara kimanin naira biliyan 1.95 daga siyar da fom din shugaban kasa kadai.
Yayin da wasu suka siyi fom din da kudinsu, wasu kamar su gwamnan CBN, Godwin Emefiele da shugaban AfDB, Akinwunmi Adesina, sun samu nasu ne daga wasu kungiyoyi koda dai basu riga sun ayyana kudirinsu ba tukuna.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kafin wa’adin ya cika, ana sanya ran wasu Karin yan takara za su siya nasu fom din. Sai dai, a halin yanzu, ga jerin yan takarar da suka mallaki fom dinsu.
1. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
2. Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi
3. Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi
4. Sanata Rochas Okorocha
5. Karamin ministan ilimi Chukwuemeka Nwajiuba
6. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo
7. Tsohon shugaban majalisar dattawa Ken Nnamani
8. Ministan kwadago Chris Ngige
9. Gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa
10. Tsohon kakakin majalisar wakilai Dimeji Bankole
11. Sanata Ajayi Boroffice
12. Sanata Ibikunle Amosun
13. Ministan kimiya da fasaha, Ogbonnaya Onu
14. Gwamnan babban bankin kasa (CBN) Godwin Emefiele (yak i karbar fom din)
15. Shugaban AfDB, Akinwumi Adesina
16. Gwamana Kayode Fayemi na jihar Ekiti
17. Ministan sufuri Rotimi Amaechi
18. Misis Uju Kennedy, yar takara mace daya tilo
19. Fasto Tunde Bakare
20. Fasto Nicholas Felix
Kada ku barnata kuri'unku, kawai ku zabe ni – Amaechi ga wakilan APC
A wani labarin, ministan sufuri kuma mai son zama shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Rotimi Amaechi, ya ce zabarsa a matsayin wanda zai rike tutar jam’iyyar ba zai zama asarar kuri’u ba.
Amaechi ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 8 ga watan Mayu, a yayin da yake zantawa da wakilan jam’iyyar a jihar Edo, jaridar The Cable ta rahoto.
Ya bukaci wakilan da su mayar da hankali wajen zabar dan takarara irinsa wanda ya cancanta domin daga tutar jam’iyyar.
Asali: Legit.ng