Shugaban kasa a 2023: Abubuwa 5 da ficewar Jibrin daga APC zai janyowa Tinubu

Shugaban kasa a 2023: Abubuwa 5 da ficewar Jibrin daga APC zai janyowa Tinubu

Yan Najeriya musamman masu sharhi kan harkokin siyasa sun cika da mamaki a ranar Asabar, 7 ga watan Mayu, lokacin da suka ji cewa shugaban kungiyar kamfen din Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Abdulmunin Jibrin, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Tun bayan nan, ana ta tattaunawa kan abun da hakan ke nufi ga siyasar babban jagoran jam’iyyar mai mulki na kasa wanda ke son darewa kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Legit.ng ta tattaro akalla abubuwa biyar da sauya shekar Jibrin zai janyo gabannin zaben fidda gwani na APC da ma zaben shugaban kasa mai zuwa.

Shugaban kasa a 2023: Abubuwa 5 da ficewar Jibrin daga APC zai janyowa Tinubu
Shugaban kasa a 2023: Abubuwa 5 da ficewar Jibrin daga APC zai janyowa Tinubu Hoto: @tsg2023, Abdulmumin Jibrin
Asali: Facebook

1. Ayar tambaya kan APC

Ko shakka babu wannan hukunci na Jibrin ya dasa ayar tambaya kan jam’iyyar mai mulki wacce ke ikirarin lashe kusan dukkanin kujeru a zaben 2023, ciki harda na shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Hakazalika, wannan sauya shekar ya dasa ayar tambaya na, ta yaya jam’iyyar APC ta warware rikicin cikin gidanta da kuma tausar fusatattun mambobinta a kasar?

2. Shugabancin Tinubu

Haka kuma, akwai shakku kan ko Tinubu zai cimma kudirinsa na son zama shugaban kasa yayin da babban baraka na farko ya kunno kai a jam’iyyar kafin zaben.

Ya zama dole Jagaban ya kara kaimi sosai don tabbatarwa duniya irin karfin da yake da shi a APC da kuma tasirinsa a arewa.

Idan har yunkurin sasanci da Tinubu ke son yi tsakanin Gwamna Abdullahi Ganduje da Jibrin bai haifar da ‘ya’ya masu idanu ba kamar yadda ake sanya rai, abubuwa da yawa na iya kwabe masa.

3. Tinubu na iya rasa farin jininsa a arewa

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Tinubu ya samu 'delegate' 370, ya mika fom dinsa na takarar gaje Buhari

Abubuwa na iya kwabewa tsohon gwamnan na jihar Kano idan ana magana kan yankin arewa, kasancewar Jibrin ya fito daga Kano, jihar da a cikinta ne Tinubu ya shahara kuma yake da masoya.

Abu mai sauki ne amma kuma babba a zahiri: idan dan siyasa mai karfi kamar Jibrin wanda yake dan asalin wannan jiha ta arewa wacce APC ke da karfi a cikinta zai iya barin jam’iyyar a daidai wannan lokaci, toh lallai Tinubu na iya kasancewa a hanyar rasa farin jininsa a yawancin yankunan shiyar.

4. Babban dama ga PDP

Ko shakka babu jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ba za ta bari wannan damar ta wuce ta ba. Tabbaci ne cewa babbar jam’iyyar adawa ta kasar za ta yi amfani da wannan rikicin gaba daya a kamfen dinta.

Balle ma ace, idan Jibrin ya sauya sheka zuwa PDP, zai zama dabara kan dabara lokacin da gangamin kamfen din shugaban kasa zai fara sosai gabannin 2023.

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Abubuwa 5 da Tinubu ya ce zai yiwa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

5. Osinbajo na iya zama mafita

Idan duk wadannan basu yi ba, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo na iya zama mafita na gaba. Duba ga yanayi da dama, Osinbajo ne babban dan takarar shugaban kasa na APC bayan Tinubu.

Mataimakin shugaban kasar da kansa ya bayyana cewa Allah ya dora shi a kujerar mulki domin ya yi amfani da tarin gogewarsa idan ya zama shugaban kasa a 2023.

2023: Tinubu ya saka baki a rikicin APC a Kano bayan Jibrin ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar

A gefe guda, mun ji cewa babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya saka baki domin magance rikicin siyasa tsakanin Abdulmumin Jibrin da manyan masu ruwa da tsaki a mazabarsa da ke jihar Kano.

A ranar Asabar, 7 ga watan Mayu ne Jibrin ya sanar da hukuncinsa na barin jam’iyyar APC zuwa wata jam’iyya da bai bayyana ba.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Aminu Tambuwal ya nuna karfin gwiwar mallakar tikitin PDP

Jibrin bai bayar da kowani dalili da ya sanya shi yanke hukuncin barin APC ba, sai dai majiyoyi sun ce hakan na da nasaba da hukuncin hana shi tikitin komawa majalisar wakilai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel