2023: Tinubu ya saka baki a rikicin APC a Kano bayan Jibrin ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar

2023: Tinubu ya saka baki a rikicin APC a Kano bayan Jibrin ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar

  • Jam’iyyar APC reshen jihar Kano na fama da matsala yayin da darakta janar na kamfen din Tinubu, Abdulmumin Jibrin ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar
  • An tattaro cewa an dade ana fama da rikici tsakanin Jibrin da gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje
  • Majiyoyi sun bayyana cewa Asiwaju Tinubu ya shiga lamarin kuma ana sanya ran za a magance matsalar nan ba da dadewa ba

Kano - Babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya saka baki domin magance rikicin siyasa tsakanin Abdulmumin Jibrin da manyan masu ruwa da tsaki a mazabarsa da ke jihar Kano.

A ranar Asabar, 7 ga watan Mayu ne Jibrin ya sanar da hukuncinsa na barin jam’iyyar APC zuwa wata jam’iyya da bai bayyana ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

2023: Tinubu ya saka baki a rikicin APC a Kano bayan Jibrin ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar
2023: Tinubu ya saka baki a rikicin APC a Kano bayan Jibrin ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar Hoto: Abdulmumin Jibrin
Asali: Facebook

Jibrin bai bayar da kowani dalili da ya sanya shi yanke hukuncin barin APC ba, sai dai majiyoyi sun ce hakan na da nasaba da hukuncin hana shi tikitin komawa majalisar wakilai.

Akwai sabani tsakanin Jibrin da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, na tsawon lokaci yanzu kan lamuran da suka shafi siyasarar jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jibrin ya wakilci mazabar Kiru/Bebeji a majalisar wakilai tsakanin 2011 da 2019 kafin ya sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar PDP a zaben da aka sake a 2020.

TVC News ta rahoto daga majiya cewa Tinubu ya tuntubi Gwamna Ganduje domin ganin an sasanta da kuma kokarin ganin hadin kan Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano bai wargaje ba.

Majiyar ta ce tuni Tinubu ya shiga lamarin a madadin Jibrin da Gwamna Ganduje kuma za a warware komai.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Tinubu ya samu 'delegate' 370, ya mika fom dinsa na takarar gaje Buhari

“Jibrin zai je ganin Tinubu. Tinubu ya shiga lamarin. Jibrin na fama da matsalolin cikin gida da mazabarsa da Ganduje. Za a magance komai.”

Wani makusancinsa da ya nemi a sakaya sunansa ya fadama jaridar The Guardian cewa Jibrin ya yi furucin ne saboda sabon shiri da jam’iyyar ke yi na hana shi tikiti.

Majiyar ta bayyana cewa Jibrin ya samu labarin cewa Gwamna Ganduje na shirin kawo masa cikas a karo na biyu.

Diraktan kamfen Tinubu, AbdulMumini Jibrin, ya fita daga jam'iyyar APC

A baya mun ji cewa Shugaban majalisar kungiyoyin kamfen dan takaran shugaban kasa, Bola Tinubu, Hanarabul Abdulmumini Jibrin ya sanar da fitarsa daga jam'iyyar All Progressives Congress APC.

AbdulMumini Jibrin a jawabin da ya saki a shafukansa na ra'ayi da sada zumunta yace lokaci ya yi da zai hakura da APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel