2023: Gwamna Masari ya yabi ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP kan abu ɗaya

2023: Gwamna Masari ya yabi ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP kan abu ɗaya

  • Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Ƙatsina ya yabi takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike, kan matakin da ya ɗauka game da IPOB
  • Gwamnan ya ce ba zai taɓa mancewa da goyon bayan da mutan Ribas suka ba shi ba lokacin yana kakakin majalisar wakilai
  • Wike ya kai wa Masari ziyara ne domin sanar da shi aniyarsa ta neman shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa

Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya yabi takwaransa na jahar Ribas, gwamna Nyesom Wike, bisa jajircewarsa wajen dunƙulewar Najeriya.

A rahoton Vanguard, Gwamna Masari ya bayyana cewa Wike ya yi namijin kokari wajen daƙile yaɗuwar haramtacciyar ƙungiyar yan aware IOPB zuwa cikin jihar Ribas.

Masari, wanda ya nuna jin daɗinsa da ganin mutane kamar gwamna Wike sun ayyana sha'awar jan ragamar Najeriya, ya ce hakan alama ce dake nuna haɗin kai ya samu gindin zama a ƙasa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da Buhari, Wani Minista ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa

Gwamna Masari da Wike.
2023: Gwamna Masari ya yabi ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP kan abu ɗaya Hoto: PDP Media Vanguard/facebook
Asali: Facebook

Gwamna ya yi wannan kalaman yabon ne ranar Talata lokacin da Wike ya kai masa ziyara da nufin sanar da shi kudirinsa na neman takarar shugaban ƙasa a zaɓen mai zuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamasan, Masari ya ce:

"Abun godiya ne ga Allah ganin mutum kamar ka daga Ribas yana niyyar zama shugaban ƙasa, haka wata alama ce dake nuna ƙasar mu ta kama hanyar zama dunƙulalliya."
"A karan kaina na yaba wa rawar da ka taka a matsanancin lokacin yan IPOB, na san jajircewar da ka yi a matsayin ɗan Najeriya. Da ka bar abun ya watsu cikin Ribas da Allah kaɗai ya san halin da muke ciki yanzu."
"A koda yaushe ina maraba da kai a nan, kai aboki ne kuma ɗan uwa, wanda zamu iya cin abinci tare duk da inuwar mu ta banbanta amma zamu ci abinci tare da juna."

Kara karanta wannan

Zaura ya bi zabin Ganduje ya janye daga takarar gwamnan Kano, zai kwace kujerar Shekarau a 2023

Ba zan manta da mutanen Ribas ba - Masari

Bayan haka, gwamna Masari ya ƙara da cewa yana ji a jikinsa wajibi ne ya tarbi duk wanda aka ce ya fito daga jihar Ribas saboda tsantsar goyon bayan da ya samu daga jihar lokacin ya na kakakin majalisar wakilai.

"Idan akwai wata jiha da zance ta ba ni goyon baya 100 bisa 100 a lokacin da nake kakakin majalisa to Ribas ce, shiyasa har yanzun akwai ƙawance tsakanin mu."
"Bisa haka, duk wanda aka ce ɗan jihar Ribas ne a kowane mataki nake ko matsayi a shirye nake ta tarbe shi zuwa gida na."

A wani labarin kuma Shugaban kasa a 2023: Jerin sunayen waɗan da suka sayi Fom da masu shirin saye kan Miliyan N100m a APC

A ranar 6 ga watan Mayu, 2022, jam'iyyar APC ta tsara rufe Siyar da Fom ɗin nuna sha'awa da tsayawa takara a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

2023: Ministan Man Fetur da wani gwamnan APC sun karɓi Fom, sun shiga takarar shugaban ƙasa

Shugaban majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, da ɗan kasuwa Olawepo Hashim sun shirya shiga tseren, APC zata iya tara N2bn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel