Shugaban kasa a 2023: Jerin sunayen waɗan da suka sayi Fom da masu shirin saye kan Miliyan N100m a APC

Shugaban kasa a 2023: Jerin sunayen waɗan da suka sayi Fom da masu shirin saye kan Miliyan N100m a APC

  • A ranar 6 ga watan Mayu, 2022, jam'iyyar APC ta tsara rufe Siyar da Fom ɗin nuna sha'awa da tsayawa takara a zaɓen 2023
  • Shugaban majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, da ɗan kasuwa Olawepo Hashim sun shirya shiga tseren, APC zata iya tara N2bn
  • Tuni wasu yan takarar suka biya kuma suka karɓi Fom wasu kuma na shirin siya, da yuwuwar masu sha'awa su kai 20

Abuja - Yayin da wa'adin sayar da Fom na APC ke gab da ƙarewa, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, fitaccen ɗan kasuwa, Gbenga Olawepo-Hashim, na shirin lale N100m su sayi Fom ɗin takarar shugaban kasa.

Daily Trust ta ce zuwa yanzun yan takara Shida sun karbi Fom bayan biyan N100m, sun haɗa da, Bola Tinubu, Gwamna Yahaya Bello na Kogi da gwamna Dave Umahi na Ebonyi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Goodluck Jonathan ba zai yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ba

Sauran sune; ƙaramin ministan Ilimi, Emeka Nwajiuba, Sanata Rochas Okorocha, sai kuma yar takara mace, Uju Kennedy, wacce ta karbi Fom ɗin bayan biyan N30m bisa umarnin APC.

Yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Shugaban kasa a 2023: Jarin sunayen waɗan da suka sayi Fom da masu shirin saye kan Miliyan N100m a APC Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Bisa jadawalin da jam'iyyar APC ta fitar, wa'adin sayar da Fom ɗin nuna sha'awa da tsayawa takara zai kare ne ranar 6 ga watan Mayu, 2022.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa jam'iyya mai mulki ka iya tara Biliyan biyu daga yan takara 20 da suka nuna sha'awar neman kujera lamba ɗaya a Najeriya.

Yan takarar na hangen kujerar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda wa'adin mulkinsa zango na biyu zai kare a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Jerin mutanen da zasu Sayi Fom nan gaba

Ministan Neja Delta, Godswill Akpabio, ya shirya ayyana shiga tseren takara yau yayin da ake zaton tsohon gwamnan Akwa Ibom, zai iya Sayen Fom a yau Laraba.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen Jaruman Kannywood da suka fito takara da kujerun da suke nema a 2023

Sauran yan takarar da ake tsammanin zasu karbi Fam sun haɗa, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, tsohon kakakin majalisar wakilai, Dimeji Bankole; Sanata Ibikunle Amosun, shugaban ƙungiyar gwamnoni (NGF), Kayode Fayemi.

Sauran yan takarar dake cikin tseren sune; gwamna Ben Ayade na Kuros Riba, Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, Ministan Kwadugo, Chris Ngige, Ihechukwu Dallas Chima, Usman Iwu, Tein Jack-Rich amda kuma Adamu Garba II.

Shugaban Majalisar Dattawa ya shirya karɓan Fom

Wani hadimin shugaban majalisar dattawa ya shaida wa wakilin jaridar cewa sun kammala duk wani shirye-shirye na Sanata Ahmad Lawan ya karbi Fom ɗin takara yau.

Ya ce:

"A ranar Laraba, shugaban majalisar dattawa zai karɓi Fom na takarar shugaban ƙasa. Hakan ya biyo bayan matsin lambar da yake sha daga Dattawan ƙasa."

A wani labarin kuma Daga karshe, Shugaban Buhari ya bayyana wanda zai miƙa wa Mulki a zaɓen 2023

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya ƙara magana kan wanda zai iya miƙa wa ragamar mulkin Najeriya bayan zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Zaura ya bi zabin Ganduje ya janye daga takarar gwamnan Kano, zai kwace kujerar Shekarau a 2023

Da aka tambaye shi kan haka bayan kammala Sallar Idi a Abuja, Buhari yace zai miƙa mulki ga duk wanda yan Najeriya suka zaɓa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel