Zaura ya janye daga takarar gwamnan Kano ya koma bayan Gawuna, zai kwace kujerar Shekarau a 2023

Zaura ya janye daga takarar gwamnan Kano ya koma bayan Gawuna, zai kwace kujerar Shekarau a 2023

  • AA Zaura, ɗaya daga cikin masu hangen kujerar gwamnan Kano, ya ce ya goyi bayan zaɓin Ganduje na Gawuna/Garo 2023
  • Sai dai ɗan siyasan ya ce zai tsaya takarar Sanata mai wakiltar mazaɓar Kano ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya
  • Hakan na nufin idan Shekarau zai sake neman kujerar a APC, zasu fafata a zaɓen fidda gwani a watan Mayu 2022

Kano - Ɗan takarar kujerar gwamnan Kano, AA Zaura, ya janye ya sayi Fom ɗin takarar Sanatan Kano ta tsakiya ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC.

A wata sanarwa da Ofishin Kamfen ɗinsa ya fitar ranar Talata, Zaura ya yi alƙawarin goyon bayan Nasir Gawuna da Murtala Garo, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Zaura da Gawuna.
Zaura ya janye daga takarar gwamnan Kano ya koma bayan Gawuna, zai kwace kujerar Shekarau a 2023 Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Mista Zaura ya rungumi hukuncin da gwamna Ganduje ya yanke na tsayar da mataimakinsa, Gawuna, ya zama ɗan takarar maslaha a zaɓen gwamnan da ke tafe.

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito tituna zanga-zanga tsirara kan yajin aikin ASUU

Ya ce:

"Ina farin cikin sanar da masoya da al'umma cewa bayan bin matakai, shawari, taro a yunkurin haɗa kai don tunkarar zaɓen 2023 ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ganduje, mun cimma matsaya da za su biyo baya."
"Mai girma, Dakta Nasir Gawuna shi ne ɗan takarar da zamu marawa baya a zaɓen fidda gwani na APC da ke tafe a watan Mayu, 2022 kuma Insha Allah shi jam'iyya zata tsayar takarar gwamna."
"Honorabul Murtala Garo, tsohon kwamishinan kananan hukumomi, shi zai zama mataimakin Gawuna a tafiyar. Ni kuma zan nemi kujerar Sanata a tarayyan Najeriya mai wakiltar mazaɓar Kano ta tsakiya."

Zan goyi bayan zaɓin Ganduje - Zaura

Bayan haka ya bayyana cewa ya amince ya bi bayan takarar Gawuna/Garo a zaɓen 2023 dake tafe da izinin Allah.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da Buhari, Wani Minista ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa

Mista Zaura ya ce shi ba ɗan siyasar a yi ko a mutu bane, ya shiga siyasa ne domin ba da gudummuwarsa kuma da izinin Allah Kano zata ƙara ɗaukaka.

A wani labarin kuma Daruruwan mambobin APC da PDP sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar NNPP a Kaduna

Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta ƙara karfi a jihar Kaduna yayin da take shirin tunkarar babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Mambobin manyan jam'iyyu APC da PDP mutum 1,000 sun sauya sheka zuwa NNPP a wani yankin jihar ta Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel