'Dole Sai Ka Yi Takara,' Magoya Bayan Jonathan a Kano Sunyi Tattaki, Sun Ba Shi Wa'adin Kwana 7 Ya Fito Takara

'Dole Sai Ka Yi Takara,' Magoya Bayan Jonathan a Kano Sunyi Tattaki, Sun Ba Shi Wa'adin Kwana 7 Ya Fito Takara

  • Wasu matasa a Kano karkashin Kungiyar Jonathan Support Organisation sun yi tattaki na musamman don kira ga tsohon shugaban kasa ya fito takara a 2023
  • Matasan ta bakin shugaban kungiyar Mubashir Tafida ya ce sun bawa Jonathan kwana 7 ya sanar da takararsa ko kuma su tashi matasa miliyan biyu zuwa ofishinsa su tursasa shi
  • Tafida ya ce Najeriya tana fama da matsaloli daban-daban da suka hada da talauci da fatara kuma Jonathan ne kadai zai iya warware wannan matsalolin

Kano - Wasu matasa a Kano karkashin Kungiyar Jonathan Support Organisation sun bawa tsohon shugaban kasar wa'adin kwana 7 ya fito ya sanar da shiga takarar shugaban kasa a 2023.

Daily Nigerian ta rahoto cewa matasan, sun taru a Sakatariyar Jihar Kano na Kungiyar Yan Jarida a ranar Asabar, bayan yin tattaki a wasu muhimman wurare a Kano.

Kara karanta wannan

2023: Adams Oshiomhole Ya Fayyace Gaskiya Kan Batun Takararsa Na Shugaban Kasa

'Dole Sai Ka Yi Takara,' Magoya Bayan Jonathan a Kano Sun Bashi Wa'adin Kwana 7 Ya Fito Takara
'Dole Sai Ka Yi Takara', Magoya Bayan Jonathan Sun Fito Tattaki a Titunan Kano. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matasan suna rike da fastoci da alluna masu dauke da rubutu daban-daban da ke nuna goyon bayansu ga tsohon shugaban kasar ya sake yin takara a 2023, Daily Trust ta rahoto.

Da ya ke magana a sakatariyar NUJ, Shugaban kungiyar magoya bayan Jonathan, Mubashir Tafida, ya ce suna kira ga Mr Jonathan ya bayyana takararsa cikin kwana bakwai ko kuma su tilasta masa yin takarar.

A cewar Tafida, Najeriya tana cikin mawuyancin hali kuma dan siyasa irin Jonathan ne kadai zai iya warware matsalolin kasar.

Ya kara da cewa tsohon shugaban kasar ya fito ya sanar da takararsa ko kuma matasa miliyan biyu su dira ofishinsa su tilasta masa yin takara.

Abubuwa da dama sun tabarbare a Najeriya, Jonathan kadai zai iya kawo gyara, Tafida

Ya ce tattalin arzikin kasar ya tabarbare, yunwa da talauci sun zama ruwan dare a kasar, yana mai cewa Jonathan zai iya magance matsalolin kamar yadda ya yi a mulkinsa na farko.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban APC Ya Bayyana Dalilan Saka N100m a Matsayin Kudin Fom Din Takarar Shugaban Kasa

"Tabarbarewar tattalin arziki yana shafar kowa. Ana bukatar mutum irin Jonathan domin ya gyara matsalar.
"Lokacin da ya ke shugaban kasa, akwai yunwa da talauci. Muna hannunsa. Shine babanmu, a matsayin mu na yaransa, muna kira gare shi ya fito takara ya ceci kasarnan daga wahalan da ta ke ciki," in ji shi.

Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164