2023: Shugaban APC Ya Bayyana Dalilan Saka N100m a Matsayin Kudin Fom Din Takarar Shugaban Kasa

2023: Shugaban APC Ya Bayyana Dalilan Saka N100m a Matsayin Kudin Fom Din Takarar Shugaban Kasa

  • Sanata Abdullahi Adamu, Shugaban Jam'iyyar APC na kasa ya bayyana dalilan da yasa jam'iyyar ta saka N100m matsayin kudin shiga neman takara.
  • Ya ce takarar shugaban kasa ba neman kujerar sarkin gari bane ko kuma shugaban tasha don haka dole a saka kudi don girma da muhimmanin kujerar
  • Ya kuma ce duk dan takarar da ke da magoya baya za su iya tara masa kudin kana idan kudin ya yi kasa sosai yan adawa za su iya biya wa wasu shedanu don kawo wa jam'iyyar cikas

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya ce jam'iyyarsa tasa Naira miliyan 100 a matsayin kudin fom din takara ne saboda muhimmancin ofishin, rahoton Premium Times.

Jam'iyyar ta sanar da farashin ne yayin taron kwamitin shugabanninta da Shugaba Muhammdu Buhari ya hallara a Abuja gabanin zaben shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Kuri'u miliyan 11 ke jirana: Atiku ya bayyana yadda 'yan Najeriya ke kaunarsa

2023: Shugaban APC Ya Bayyana Dalilan Saka N100m a Matsayin Kudin Fom Din Takarar Shugaban Kasa
2023: Dalilin Saka N100m Don Takarar Shugaban Kasa, Shugaban APC Ya Magantu. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Yan Najeriya musamman a dandalin sada zumunta sun yi gaggawar sukar jam'iyyar suna mai cewa kudin fom din takarar ya yi tsada sosai.

Sai dai cikin wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba a Muryar Amurka, VOA, da Legit.ng Hausa ta gani, ya ce masu sukar batun yan adawa da ke neman bata wa jam'iyyar suna.

Adamu ya ce takarar shugabancin Najeriya ba takarar shugaban tashar mota bane ko sarkin gari.

"Idan dan takarar shugaban kasa ba zai iya tattara masoyansa su tara masa kudin ba, toh lallai bai kamata ya shiga takarar ba tunda farko," in ji Adamu.

Ya kara da cewa:

"Shugabancin Najeriya muke magana da sarkin garinku ba. Yanzu idan sarkin garinku ya mutu mai son maye gurbinsa sai ya kashe fiye da N100m a masarauta kadai kaacal."

Kara karanta wannan

Kowa tashi ta fishe shi: Shugaban PDP ya nunawa Atiku ba sani ba sabo

Baya ga haka, Adamu ya ce akwai shugabanci da dama da ake kashe fiye da N100m kafin a samu.

Ya ce idan mutum yana takarar shugaban kasa a Amurka, magoya bayansa za su tara masa kudin da har zai iya fin na fom din takarar.

"Misali, idan wanda ke son takarar shugaban kasa ya bukaci kowanne cikin masoyansa 10,000 ya bada gudunmawar N10,000, nawa kenan zai samu?. Idan ko bai da masoya toh bai kamata ya yi takara ba. Bana son raina ka amma shugaban kasa ba sarkin garin ku bane ko shugaban tasha."

Adamu ya ce takarar ba dole bane don haka duk wanda ba shi da kudin ya hakura yana mai cewa babu wata kasa irin Najeriya da za ta saka kudin takarar ta na shugaban kasa kan N100m.

Wani dalili kuma da Adamu ya bada shine idan aka saka kudin fom din ya yi kasa sosai, yan adawa za su iya daukan nauyin wasu yan takarar domin shuka shegantaka ko fitina a garken masu takarar shugaban kasar.

Kara karanta wannan

2023: Yahaya Bello Ya Shige Gaban Su Tinubu, Ya Fara Biyan N100m Lakadan Kuɗin Fom Ɗin Takara

Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.

Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel