2023: Adams Oshiomhole Ya Fayyace Gaskiya Kan Batun Takararsa Na Shugaban Kasa

2023: Adams Oshiomhole Ya Fayyace Gaskiya Kan Batun Takararsa Na Shugaban Kasa

  • Comrade Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC, na kasa ya magantu kan takarar shugabancin kasa na 2023
  • Wasu yan jarida da masu ruwa da tsaki sun samu takarda cewa su hallarci taron kaddamarwar Oshiomhole ranar Juma'a amma suka tafi wurin ba a yi taron ba
  • Daga bisani, Adams Oshiomhole ya fayyace cewa bai kira taron kaddamar da takara ba kuma idan har zai yi toh kai tsaye zai yi magana da yan Najeriya ya sanar da su

Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Comrade Adams Oshiomhole ya yi martani kan rahotanni a dandalin sada zumunta game da shigarsa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Da ya ke magana da Vanguard, tsohon gwamnan na Jihar Edo ya ce duk lokacin da ya yi niyyar shiga takarar wani ofishi, zai yi magana da yan Najeriya kai tsaye.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Sanatan APC Okorocha ya karbi fom din takarar shugaban kasa a zaben 2023

2023: Adams Oshiomhole Ya Fayyace Gaskiya Kan Batun Takararsa Na Shugaban Kasa
2023: Oshiomhole Ya Karyata Cewa Zai Yi Takarar Shugaban Kasa. Hoto: The Nation.
Asali: Twitter

An aike wa yan jarida da masu ruwa da tsaki takardar gayyata wurin kaddamar da takarar Oshiomhole

An aike wa wasu yan jarida da wasu masu ruwa da tsaki takardar gayyata a safiyar ranar Juma'a, ana bukatar su hallarci taron kaddamar da takarar shugaban kasa na Oshiomhole a Cibiyar Al'adu a Arewa 10, Abuja.

An kuma lika manyan fostocin takarar shugaban kasa na tsohon shugaban kungiyar kwadagon a wasu manyan titunan Abuja.

Wasu daga cikin magoya bayansa sun yi tururuwa zuwa wurin da aka gayyace su amma bayan sun isa aka ce musu ba za a yi taron ba.

Watiila kuskure ne, idan zan yi takara zan sanar da mutane da kai na, Oshiomhole

Da Saturday Vanguard ta tuntube shi, Oshiomhole ya ce:

Kara karanta wannan

Wasu jiga-jigan APC sun saya wa Tinubu fom din takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC

"Bisa dukkan alamu kuskure ne, "Ba zan ayyana takara ta a jarida ba ba. Idan zan yi takara, mutane sun yi magana da su kai tsaye."

Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.

Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel