'Karin Bayani: 'Dan Majalisar Kano Ya Yi Watsi Da Kwankwasiyya, Ya Fice Daga PDP Ya Koma APC

'Karin Bayani: 'Dan Majalisar Kano Ya Yi Watsi Da Kwankwasiyya, Ya Fice Daga PDP Ya Koma APC

  • Salisu Gwangwazo, dan Majalisar Jihar Kano mai wakiltan Kano Municipal ya, kuma dan tafiyar Kwankwasiyya, ya fice daga jam'iyyar PDP ya koma APC.
  • Gwangwazo wanda aka fi sani da Alhajin Baba ya ce rarrabe-rarraben da ake samu a PDP a matakin jiha da kasa ne yasa ya fice ya koma APC.
  • Gwangwazo ya sanar da fitarsa ne cikin wasikar da ya aike wa Kakakin Majalisar Jihar Kano Hamisu Chadari a ranar Juma'a

Jihar Kano - 'Dan Majalisar Jihar Kano mai wakiltan Kano Municipal, Salisu Gwangwazo, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP ya kuma koma APC.

Daily Nigerian ta rahoto cewa Gwangwazo da aka fi sani da Alhajin Baba, ya sanar da sauya shekarsa ne cikin wata wasika da ya aike wa Kakakin Majalisar Kano, Hamisu Chadari, a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Bakano ya rasa ransa bayan ya shiga masai tsamo wayarsa da ta fada

'Dan Majalisar Kano Ya Yi Watsi Da Kwankwasiyya, Ya Fice Daga PDP Ya Koma APC
'Dan Majalisar Jihar Kano Ya Yi Watsi Da Kwankwasiyya, Ya Fice Daga PDP Ya Koma APC. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwangwazo ya ce rikicin da ake yi a PDP yasa ya fice

Sanarwar da babban sakataren watsa labarai, na Majalisar Jihar Kano, Uba Abdullahi ya ce dan majalisar ya fice daga PDP ne saboda rikicin da ake fama da ita.

"Dan majalisar ya ce ya sauya shekar ne saboda jam'iyyar PDP ta tsage biyu a jihar da kuma tarayya, wanda hakan ya ce ba zai bada damar jam'iyyar ta gudanar da ayyukanta ba, hakan yasa ya fice," a cewar wani sashi na sanarwar.

A cewar sanarwar, Kakakin majalisar ya taya Gwangwazo murnar shigowa APC ya kuma bashi tabbacin cewa za a yi masa adalci tare da mutanensa.

Idan za a iya tunawa, Gwangwazo ya rike mukamin ciyaman a karamar hukumar Kano Municipal kafin a zabe shi ya wakilci Kano Municipal a Majalisar Jihar a 2011, karkashin Jam'iyyar ANPP, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Allah ya yiwa hamshakin attajiri a Kano, Tahir Fadlullah rasuwa

Ya sha kaye a zaben 2015 lokacin da ya koma PDP ya nemi tazarce, tare da tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau.

An kuma sake zabensa a 2019 karkashin PDP lokacin da ya raba jiha da Shekarau ya shiga tafiyar Kwankwasiyya.

Yusuf I Sharada ya magantu kan komawar Gwangwazo zuwa APC

Legit.ng ta tuntubi wani jigo a tafiyar Kwankwasiyya, kuma dan takarar kujerar majalisar dokokin tarayya na Kano Municipal karkashin jam'iyyar NNPP, Yusuf I. Sharada game da ficewar Gwangwazo daga PDP zuwa APC.

Bayan sake tabbatar da sahihancin labarin sauya shekan, Sharada ya ce dama Gwangwazo ya dade da fara ja da baya daga harkokin tafiyar Kwankwasiyya don ya dade baya hallartar taruruka da wasu abubuwan na taimakawa harkar.

Ya cigaba da cewa shi Gwangwazon ba wani abu ya kare tafiyar da shi ba kuma babu wani cikin yan Kwankwasiyya da ya bi shi illa mutanensa dama da suke tare da shi.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda 'Yan Sanda Suka Tisa Ƙeyar Ɗan Takarar Gwamna Na PDP Da Wike Ya Ayyana Nemansa Ruwa a Jallo

Dama ita Kwankwasiyya haduwa ce ta mutane da suka yarda da suka yi imani da akidu irin ta shugaban tafiyar.

Da ya ke amsa tambaya kan har yanzu akwai wata alakar siyasa tsakaninsu, Sharada ya ce:

"Eh, tunda shi yanzu ya tsallaka yana can APC, mu kuma muna cikin jam'iyyar NNPP (mai kayan dadi), don mu tsarinmu ta Kwankwasiyya tsari na da muke biyayya ga jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, idan mutum ya yarda da wannan, yana Kwankwasiyya idan ba haka ba, babu wata alaka ta siyasa tsakanin mu."

Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ni 'dan Malamin addini ne, bana neman mulki, sai dai a rokeni in yi : Malami

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel