Bidiyon Yadda 'Yan Sanda Suka Tisa Ƙeyar Ɗan Takarar Gwamna Na PDP Da Wike Ya Ayyana Nemansa Ruwa a Jallo

Bidiyon Yadda 'Yan Sanda Suka Tisa Ƙeyar Ɗan Takarar Gwamna Na PDP Da Wike Ya Ayyana Nemansa Ruwa a Jallo

  • Jami'an yan sanda a Jihar Rivers sun kama dan takarar gwamna na PDP, kuma dan majalisar jiha, Honarabul Farah Dagogo
  • Hakan na zuwa ne bayan Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers ya ayyana nemansa ruwa a jallo kan zargin tada rikici
  • Wike ya yi zargin cewa Dagogo ya dakko yan kungiyar asiri sun kai hari wurin tantance yan takarar majalisa amma Dagogo ya musanta

Jihar Rivers - Tawagar yan sanda sun kama dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party a Jihar Rivers, Farah Dagogo a yammacin ranar Alhamis, rahoton The Punch.

Dagogo, wanda a yanzu dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Degema-Bonny ya siya tikitin takararsa a sakatariyar PDP da ke jihar.

Da Ɗumi-Ɗumi: Ƴan Sanda Sun Kama Ɗan Takarar Gwamnan PDP a Rivers
'Yan Sanda Sun Kama Ɗan Takarar Gwamnan PDP a Rivers. Hoto: The Nation.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An tsaurara matakan tsaro yayin da yan takara suka fara dira Sakatariyar PDP

Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, cikin sanarwar da hadiminsa, Kelvin Ebiri ya fitar ya yi ikirarin cewa Hon, Dagogo ya jagoranci yan kungiyar asiri don kai hari wurin da ake tantance yan takarar majalisar jiha da tarayya a ranar Laraba, amma Dagogo ya musanta zargin.

Yadda yan sandan suka kama Farah Dagogo

Farah ya isa sakatariyar bayan karfe 6 na yamma ya shiga inda ake tantance yan takarar, amma wasu yan sanda suna bi sahunsa.

Bayan yan mintuna, an hangi Dagogo na fitowa kewaye da jami'an tsaro dauke da makamai, suka fita da shi zuwa wata motar sintiri mai rubutun 'Operation C41-027'.

Nan take motar sintirin ta juya cikin gaggawa, a yayin da wasu jami'an tsaro suka shiga bayan motar kuma direban ya tada motar ya yi gaba.

Ga bidiyon yadda jami'an yan sandan suka tisa keyar Dagogo zuwa mota suka tafi da shi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An ji muryar wani dan majalisar tarayya na PDP na barazanar kashe wani

Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel