2023: An Tura Wa Jonathan Wasiƙa Ya Koma APC, Ya Kuma Siya Fom Ɗin Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa
- An bai wa Goodluck Ebele Jonathan wa’adin mako daya ya koma jam’iyyar APC sannan ya siya tikitin tsayawa takarar shugaban kasa na zaben 2023
- Kungiyar Harkokin Matasan Najeriya, YNNU, ce ta ba shi wannan wa’adin a ranar Laraba, 27 ga watan Afirilun 2023
- Shugaban YNNU, Ibrahim Saiki, ya shaida yadda kungiyar ta rubuta wa tsohon shugaban kasar wasika tana bukatar hakan a wajensa
Yayin da zaben shugaban kasar Najeriya na 2023 ke kara matsowa, Kungiyar Harkokin Matasan Najeriya (YNNU) ta rubuta wasika ga tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan tana bukatar ya koma jam’iyyar APC.
Shugaban YNNU na kasa, Ibrahim Saiki, a ranar Laraba, 27 ga watan Afirilu ya shaida yadda kungiyar ta aika wa Jonathan da wasika tana bukatar ya yi rijistar jam’iyyar APC a gundumar Otuoke da ke Bayelsa sannan ya siya fom din tsayawa takarar shugaban kasa na 2023, PM News ta ruwaito.
Saiki ya shaida yadda kungiyar ta bai wa tsohon shugaban kasar wa’adin mako daya bayan watan Ramadan, Nigerian Tribune ta kara.
A cewarsa, in har Jonathan ya gaza yin hakan, mambobin kungiyar za su je har ofishinsa da ke Abuja su mamaye shi har sai ya yanke shawarar.
Kamar yadda Saiki ya shaida:
“Muna mika rokonmu da bukatarmu ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan akan yin gaggawar komawa jam’iyyar APC a gundumarsa ta Otuoke da ke Bayelsa cikin kwana 7 bayan watan Ramadan.
“In har kwanakin suka kare kuma Jonathan bai dauki wani mataki ba, za mu yi abinda ya dace ta hanyar zuwa ofishinsa don yin taro ba biyu.
“Abin kula anan shi ne yadda fiye da mutane 20,000 cikin manyan mambobin kungiyarmu 500,000 da ke kasar nan suke a shirye da su shiga dumu-dumu kuma su mamaye ofishin Jonathan. Sannan zamu ci gaba da zama har sai ya bayyana mana matakin da ya dauka.”
Saiki ya ce YNNU tana fatan Jonathan zai fahimci cewa ci gaban Najeriya ya dogara ne da matakin da zai dauka.
Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja
A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.
Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.
Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.
Asali: Legit.ng