Kuri'u miliyan 11 ke jirana: Atiku ya bayyana yadda 'yan Najeriya ke kaunarsa

Kuri'u miliyan 11 ke jirana: Atiku ya bayyana yadda 'yan Najeriya ke kaunarsa

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa shi yafi cancanta ya mallaki tikitin shugaban kasa na PDP
  • Atiku ya bugi kirjin cewa shine zai iya kawowa jam’iyyar tasa kujerar shugaban kasa don a yanzu haka kuri’u miliyan 11 na nan suna jiransa
  • Dan siyasar ya kuma sha alwashin magance matsalolin tsaro, tattalin arziki da kuma hada kan kasar idan har ya samu darewa kujerar Buhari

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bukaci jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ta bashi dama a zaben fidda dan takararta na shugaban kasa saboda shine dan takara mafi cancanta da zai kawo mata kujerar.

Da yake jawabi ga mambobin kwamitin NWC na jam’iyyar a ranar Alhamis, 28 ga watan Afrilu, Atiku ya ce ya kamata a yi la'akari da shi saboda tuni ya mallaki kuri’u miliyan 11 da ke jiransa, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kowa tashi ta fishe shi: Shugaban PDP ya nunawa Atiku ba sani ba sabo

Kuri'u miliyan 11 ke jirana: Atiku ya bayyana yadda 'yan Najeriya ke kaunarsa
Kuri'u miliyan 11 ke jirana: Atiku ya bayyana yadda 'yan Najeriya ke kaunarsa Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Atiku ya ce:

“Ni ne dan takara mafi cancanta. A tashin farko Mista Ciyaman, wannan mutum ne wanda kuri’u miliyan 11 ke jiransa. Kuma ina ganin, a matsayin jam’iyya, ya kamata ku bani dama a tashin farko amma muna a tsari ne na damokradiyya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Abun da zan bukace ka shine ka tabbatar da ganin cewa ka ci gaba a yadda ka fara, ka kuma kammala ta hanyar zama adali, mai gaskiya da kuma ba dukkanin yan takara damar fuskantar masu zabe.”

Ya bukaci yan Najeriya da su tsammaci shugabanci nagari daga PDP, duba ga yadda kwamitin NWC ke gudanar da harkokin jam’iyyar.

Ya kara da cewa:

“Mu dukka mun san cewa APC ta gaza amma kada mu wofantar dadauki yan Najeriya ba a bakin komai ba. Duk mu fita mu sanar da su APC ta gaza kuma PDP bata gaza ba idan aka daura mu a ma’auni guda. Idan ka kwatanta nasarorin PDP da gazawar APC, za ka san cewa baka da wani zabi sama da PDP."

Kara karanta wannan

Kai Abokina Ne Amma Ba Zan Maka Aiki Ba, Shugaban PDP Ya Faɗa Wa Atiku

A kan tanadin da yake yiwa kasar, Atiku ya yi alkawarin ba jihohi karin iko da albarkatun kasa “saboda Ina ganin hanya mafi dacewa da za a kawo ci gaba a Najeriya shine ba bangarori daban daban damar cin gashin kansu.”

Wazirin na Adamawa ya kuma bayyana cewa idan aka zabe shi, ba zai zama shugaban kasa irin Muhammadu Buhari ba, jaridar Punch ta rahoto.

Ya yi zargin cewa shugabancin Buhari ya gaza ba ma’aikatu da hukumomi umurnin abubuwan da za su yi domin magance matsalolin tsaron kasar.

Ya ce:

“Kimanin watanni biyu da suka wuce, na kai ziyara jihar Neja, na yanke shawarar kai ziyarar ban girma ga gwamnan.
"Gwamnan ya fada mani cewa muna da kimanin kananan hukumomi goma sha biyu da ke karkashin ikon yan bindiga. Ba mu san ya za mu gudanar da zabe a wadannan kananan hukumomi ba. Kuma na je wajen shugaban kasa na ce masa muna bukatar karin yan sanda sai Shugaban kasar ya ce ta yaya zan baku karin yan sanda alhalin Inspekto janar na yan sanda da hukumar yan sanda suna kotu kan wanda zai dauki yan sanda aiki.

Kara karanta wannan

Ba na jin tsoron kowa a APC, Yahaya Bello ya karfafi rade-radin takarar Jonathan a 2023

“Ba zan taba zama irin wannan Shugaban kasar ba. Ba za mu iya daukar yan sanda ba sabida hukumomin biyu na a kotu sannan muna da shugaban kasa da ba zai iya saita shugabannin hukumominsa ba, ba ma ministoci ba."

Kowa tashi ta fishe shi: Shugaban PDP ya nunawa Atiku ba sani ba sabo

A gefe guda, Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, Dr. Iyorchia Ayu, ya fada ma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, cewa duk da cewar su abokai ne, ba zai taba yi masa aiki a matsayinsa na dan takara ba.

Daily Trust ta rahoto cewa, Ayu, ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi ga mambobin kwamitin NWC da tawagar kamfen din tsohon mataimakin shugaban kasar bayan wata ziyara da suka kai sakatariyar jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng