Kowa tashi ta fishe shi: Shugaban PDP ya nunawa Atiku ba sani ba sabo

Kowa tashi ta fishe shi: Shugaban PDP ya nunawa Atiku ba sani ba sabo

  • Shugaban jam'iyyar PDP na kasa ya fada ma Atiku Abubakar cewa duk da kasancewarsu aminan juna, zai yi aikinsa ne babu sani babu sabo
  • Ayu ya dauki alkawarin cewa zai yi adalci a tsakanin dukkanin yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawar guda 17
  • Ya bayyana hakan ne a lokacin da tsohon mataimakin shugaban kasar ya kai ziyara hedkwatar jam'iyyar da ke Abuja

Abuja - Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, Dr. Iyorchia Ayu, ya fada ma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, cewa duk da cewar su abokai ne, ba zai taba yi masa aiki a matsayinsa na dan takara ba.

Daily Trust ta rahoto cewa, Ayu, ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi ga mambobin kwamitin NWC da tawagar kamfen din tsohon mataimakin shugaban kasar bayan wata ziyara da suka kai sakatariyar jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Ba na jin tsoron kowa a APC, Yahaya Bello ya karfafi rade-radin takarar Jonathan a 2023

Kowa tashi ta fishe: Shugaban PDP ya nunawa Atiku ba sani ba sabo
Kowa tashi ta fishe: Shugaban PDP ya nunawa Atiku ba sani ba sabo Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Ayu ya kuma bayyana godiyar jam’iyyar ga Atiku kan yadda ya taimaka wajen samar da sakatariyar PDP ta kasa a lokacin da yake kan mulki, rahoton Vanguard.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Bari na fayyace gaskiya cewa ni da kai abokai ne na kut-da-kut tsawon sama da shekaru 30 kamar yadda ya nuna, mun kasance manyan jiga-jigai a jam’iyyar Social Democratic Party kuma jiga-jigai a wajen fitowar Cif MKO Abiola.
“Don haka kai dan takarar shugaban kasa ne a yau. Amma ina so mutane su sani cewa har yanzu kai abokina ne. Ba zan karyata haka ba bana taba karyata abota na da mutum ciki harda wadanda ke wasu jam’iyyar. Ka san su saboda don ko a da chan abokanmu daya wadanda suka kauce hanya, wadanda da ya kamata ace suna nan tare da mu.

Kara karanta wannan

Ramadan: Tinubu, Nyako da jiga-jigan APC 15 da za su yi buda baki tare da Buhari a yau

“Abu mafi muhimmanci, tunda muka kafa wannan jam’iyyar kamar yadda ka ambata, mun yi aiki tare a matakai daban-daban. Ni da kaine muka kitsa samuwar shugaban kasa Obasanjo. Gwamnati da ta yi namijin kokari, wacce ta karfafa Najeriya a bangaren tattalin arziki, zamantakewa da siyasa.
“Sannan, ba zan iya musanta gaskiyar cewa mun yi aiki tare cikin jituwa ba, imma a batutuwan siyasa ko batutuwan tattalin arziki da kuma kan kwamitin tsaron kasa lokacin ina a matsayin Ministan harkokin cikin gida.
“Ina jero wannan zantukan ne domin na fayyacewa wadanda ke cewa saboda kusancina da kai a matsayina na shugaba, zan yi maka aiki. Ya mataimakin shugaban kasa, ba zan yi maka aiki a matsayinka na dan takara ba. Zan yiwa dukkanku yan takara 17 aiki. Ya rage gareka ka tabbatarwa wakilan jam’iyyarmu cewa kaine ka fi cancanta.
“Ya zama dole ka tallata kanka, ya zama dole ka jajirce. Wannan kwamitin Aiki na kasa a yanzu mun zama na kowa. Ba za mu dauki bangare da kowani dan takara ba. Amma duk muna son ku duka. Na sha fadi cewa duk wanda aka ba dama a cikinku zai tafiyar da kasar nan fiye da abun da APC ta yi ko za ta yi.”

Kara karanta wannan

Jigon APC ga 'yan takara: Kunsan ba ku da N100m me ya kai ku takara a jam'iyyar APC

2023: Tsoffin ministocin PDP sun cimma matsaya kan yadda za su fatattaki APC

A gefe guda, mun ji cewa tsoffin ministocin da suka yi aiki a karkashin inuwar jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) na aiki domin tabbatar da ganin cewa an tsayar da yan takarar da suka cancanta don fuskantar APC a babban zaben 2023.

A yanzu haka, tsoffin ministocin sun zuba idanu sosai kan tsarin tantance dukkanin yan takarar shugaban kasa na PDP, AIT News ta rahoto.

Rahoton ya kuma kawo cewa an cimma wannan matsayar ne a wata ganawa da suka yi a daren ranar Laraba, 27 ga watan Afrilu, a Abuja duk daga cikin kokarin sanin dukkanin masu neman takarar shugaban kasa da cancantarsu wajen samar da shugabanci nagari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel