Abin Da Maƙarfi, Fayose, Da Wasu Shugbannin PDP Suka Ce Game Da Ƙishin-Ƙishin Ɗin Komawar Jonathan Zuwa APC

Abin Da Maƙarfi, Fayose, Da Wasu Shugbannin PDP Suka Ce Game Da Ƙishin-Ƙishin Ɗin Komawar Jonathan Zuwa APC

  • A yan kwanakin nan dai rahotanni sun rika yawo da ke cewa akwai yiwuwar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zai fice daga PDP ya koma APC don yin takara a 2023
  • A game da hakan ne wasu shugabannin jam'iyyar PDP da suka hada da Sanata Ahmed Makarfi, Ayo Fayose, Samuel Ortom da wasu suka tofa albarkacin bakinsu
  • Yayin da wasu daga cikinsu suka ce ba za su yi tsokaci ba domin ba su ji komai daga bakinsa ba, wasu sun nuna cewa abin fa kaman da wuya duba da dadewar da ya yi a PDP

A yayin ake cigaba da yada jita-jitar cewa tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan zai fice daga Jam'iyyar PDP ya koma APC, kawo yanzu APC bata ce komai ba; shugabannin jam'iyyar adawar ta PDP a ranar Talata sun yi magana da Vanguard game da batun.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Gwamnati za ta iya maka ASUU a kotu idan aka gagara yin sulhu inji Minista

Jonathan wanda aka zabe shi shugaban kasa a 2011 amma ya sha kaye hannun Muhammadu Buhari a 2015, ya juya wa PDP baya cikin shekaru bakwai da rabi da suka shude.

Abin Da Shugbannin PDP Suka Ce Game Da Ƙishin-Ƙishin Ɗin Komawar Jonathan Zuwa Jam'iyyar APC
Shugabannin PDP sun magantu kan jita-jitar komawar Jonathan jam'iyyar APC. Hoto: Vanguard.
Asali: Twitter

Ya rika kauracewa tarurukan jam'iyyar har da taronsu na kasa a 2017, 2018 da na 2021 inda aka zabi shugabannin jam'iyyar da ke rike mu madafan iko a yanzu da wasu tarukan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin da fastocinsa suka mamaye wasu wurare a Abuja; an rahoto cewa Jonathan yana shirin koma wa APC bayan an ce ya bukaci Shugaba Buhari ya goyi bayansa.

Martanin Sakataren PDP na kasa

A hirar da ya yi da Vanguard, Sakataren PDP na kasa Debo Ologunagba ya ce jam'iyyar ba za ta yi martani kan jita-jita ba kan ko Jonathan zai sauya sheka.

Kara karanta wannan

N50m na ware tun farko, Minista ya fadi hanyar da zai tara N100m na sayen fam a APC

"Ba za mu ce komai ba a yanzu. A sanin mu, tsohon shugaban kasar bai sauya sheka ba. Bai ce zai sauya sheka ba. Idan ba ya fice din ba, PDP ba za ta ce komai ba kan jita-jita. Mu da abin zahiri muke la'akari," in ji shi.

Martanin Gwamna Ortom na Benue

Da ya ke magana a madadin mai gidansa, Nathaniel Ikyur, Babban sakataren watsa labarai na gwamnan Jihar Benue, Samuel Orom ya ce:

"Siyasa ra'ayi ne," ya kara da cewa idan Jonathan ya koma jam'iyya mai mulki,"Ba zan ce komai a kai ba."

Abin da Makarfi ya ce game da batun sauya shekar Jonathan

A bangarensa, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi ya ce yan siyasa na da ikon aikata abin da ransu ke so a matsayinsu na mutane, go su tafi hagu ko dama.

"Rayuwarsa (Jonathan) ne," a cewar Makarfi cikin gajeruwar amsar da ya bada, alamar da ke nuna cewa tsohon shugaban kasar ya yi tafiyarsa idan yana so, jam'iyyar za ta cigaba da harkokinta.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDLEA ta kai samame wurin bikin casu a Abuja, ta cafke jama'a da yawa

Martanin Ayo Fayose

Bayan an ta masa tambayar, tsohon gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose ya ce ba zai iya tabbatarwa ko Jonathan zai koma APC ba ko akasin hakan.

"Ban san abin da ke zuciyarsa ba," in ji shi.

Abin da Tari Iberia Oliver ta ce

Ita kuma, Tari Iberia Oliver, yar takarar shugaban kasa mace tilo na PDP, ta nuna rashin gamsuwa da batun na cewa Jonathan zai fice daga PDP ya koma APC.

Kasancewarsa dan PDP tsawon shekaru 19, yar takarar shugaban kasar ta ce PDP ba za ta damu kan rahotannin ba domin Jonathan 'da kansa bai ce zai fice daga jam'iyyar ba.'

Ta cigaba da cewa:

"Ban tunanin hakan zai faru. Don haka, kada muyi magana kan abin, domin akwai yiwuwar jita-jitar za ta bace kamar yadda ta zo. Ka ka manta, muna lokacin siyasa ne kuma ana yawaita maganganun da ba gaskiya bane."

Ba A Ga Atiku Ba A Taron Da Wike Ya Yi Da Masu Neman Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar PDP

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Boko Haram: Ba zai yiwu ku dunga kashe bayin Allah kuna kabbarta 'Allahu Akbar' ba

A wani labarin, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya bai halarci taron sirrn da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya shirya ba tare da wasu ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ba, yayin da zaben fidda gwanin jam’iyyar ya ke karatowa.

An tattaro yadda ‘yan takarar suka dade suna tattaunawa dangane da wanda zai tsaya takara don gudun tashin tarzoma ta cikin jam’iyyar yayin zaben, The Nation ta ruwaito.

‘Yan takarar da suka halarci taron da aka yi gidan gwamnati da ke Port Harcourt sun hada da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed; Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon manajan darekta na bankin kasa da kasa na FSB, Dr. Mohammed Hayatu-Deen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164