Buhari ga 'yan Boko Haram: Ba zai yiwu ku dunga kashe bayin Allah kuna kabbarta 'Allahu Akbar' ba

Buhari ga 'yan Boko Haram: Ba zai yiwu ku dunga kashe bayin Allah kuna kabbarta 'Allahu Akbar' ba

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a yanzu mutane sun fara gane gaskiya cewa Boko Haram bai da ginshiki na addini ko kabila
  • Buhari ya ce babu yadda za a yi mutum ya dunga kadaita Allah sannan yana kashe bayinsa da basu ji ba basu gani ba da sunan addini
  • Ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 19 ga watan Afrilu, yayin da ya karbi bakuncin babban mai gabatar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa a Villa

Abuja- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ta’addancin Boko Haram bai da tushe na addini ko kabila kuma da isasshen ilimi, yawancin yan Najeriya sun san gaskiya a yanzu.

Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 19 ga watan Afrilu yayin da ya karbi bakuncin Karin Ahmad Khan, babban mai gabatar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) a fadar shugaban kasa da ke Abuja, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ko matarsa bata yarda da tafiyar mulkinsa ba: Fasto Kukah ya sake caccakar Buhari

Buhari ga 'yan Boko Haram: Ba zai yiwu ku dunga kashe bayin Allah kuna kabbarta 'Allahu Akbar' ba
Buhari ga 'yan Boko Haram: Ba zai yiwu ku dunga kashe bayin Allah kuna kabbarta 'Allahu Akbar' ba Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Shugaban kasar ya kara da cewa, ta hanyar wayar da kan jama’a, a yanzu mutane sun fahimci cewa Boko Haram masu ci da addini ne sabanin akidar musulunci.

A cewarsa:

“Allah adali ne. Ba za ka kashe bayin Allah da basu ji ba basu gani ba sannan ka dunga ihun ‘Allah Akbar’. Imma dai baka san Allah ba kwata-kwata, ko kuma dai kawai kai wawa ne.
“Mutum ya ce karatun Boko Haram ne yaurada ce tsantsa. Wannan ne dalilin da yasa muke yakarsu, sannan muke wayar da kan mutane. Kuma muna samun nasara sosai. Mun hau karagar mulki a lokacin da abubuwa suke yi muni matuka, amma muna wayarwa mutane da kai.
“Ilimi yana da mahimmanci. Addini da kabilanci basa daga cikinsa. Wasu mutane sun mayar da shi tsarin rayuwa don haifar da rudani, halaka da mutuwa."

Kara karanta wannan

Abin Da Yasa Har Yanzu FG Ba Ta Tura Wa Ƴan Bindiga Jiragen Yaƙin Tucano Su Ragargaje Su Ba, Fadar Shugaban Ƙasa

A nashi bangaren, mai gabatar da karar na ICC ya bayyana cewa tsattsauran ra'ayi kamar kansa ne, wanda ke yaduwa kuma yana iya komawa baya.

A cewarsa, abin da Boko Haram ke yi tare da hadin gwiwar ISWAP bata addini ne, rahoton Pulse Nigeria.

Zulum: Muna Sane Da Hatsarin Da Ke Tattare Da Shirin 'Sauya Tunanin Tubabbun Ƴan Ta'adda'

A wani labarin, Babagana Zulum, Gwamnan Jihar Borno yayin da yake amsar tubabbun ‘yan ta’adda ya ce gwamnati ba za ta makance wa hadarorin da ke tattare da shirin sabunta dabi’un tsofaffin ‘yan ta’addan ba, The Punch ta ruwaito.

A cewarsa, akwai bukatar tsananta tsaro da kuma bin hanyoyi da dama wadanda zasu cire hadarorin da ke tare da shirin, kuma su tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Gwamnan ya kwatanta tubar mayakan Boko Haram da ISWAP fiye da 35,000 a matsayin taimako daga Ubangiji sakamakon addu’o’in mutane daban-daban na duniya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari tayi magana a kan ceto Bayin Allah da aka sace a jirgin Kaduna-Abuja

Asali: Legit.ng

Online view pixel