Yajin aiki: Gwamnati za ta iya maka ASUU a kotu idan aka gagara yin sulhu inji Minista

Yajin aiki: Gwamnati za ta iya maka ASUU a kotu idan aka gagara yin sulhu inji Minista

  • Sanata Chris Ngige bai da masaniya a kan yaushe ‘daliban jami’a za su koma kan karatu a Najeriya
  • Ministan kwadago da samar da ayyukan yi ya nemi a tambayi ASUU yaushe za ta janye yajin-aikin ta
  • Ngige ya ce bai dace malaman su rika neman budewa Ministan sadarwa da shugaban NITDA ido ba

Abuja - Ministan kwadago da samar da ayyukan yi a Najeriya, Chris Ngige ya ce gwamnatin tarayya za ta duba yiwuwar shiga kotu da kungiyar ASUU.

A ranar Alhamis, 21 ga watan Afrilu 2022, The Cable ta rahoto cewa an yi hira ta musamman da Ministan, inda ya tabo batun yajin-aikin malaman jami’o’i.

A hirarsa da gidan talabijin na Channels, Dr. Ngige ya ce dole kungiyar ASUU ta daina neman yi wa shugaban NITDA da Ministan sadarwa na kasa barazana.

Kara karanta wannan

N50m na ware tun farko, Minista ya fadi hanyar da zai tara N100m na sayen fam a APC

Chris Ngige ya ce a hakikanin gaskiya, a yanzu gwamnatin tarayya ba ta da kudin da malaman jami’a suke nema da zai sa ayi masu karin 180% a albashinsu.

Ku kyale Kashifu da Pantami - Ngige

“Mafitar ita ce, na farko dole ASUU ta sauka daga kujerar da ta ke kai. Ba za ku je ku na yi wa mutane a hukumar NITDA barazana ba”
“Ku na barazanar za ku karbe matsayin Farfesan da aka ba Ministan sadarwa, ku na cewa Farfesan bogi ne shi, ba ku amince ba.”

- Chris Ngige

Chris Ngige
Sanata Chris Ngige Hoto: www.dailypost.ng
Asali: UGC

Za a karbi rahotonsu Nimi Briggs

Ngige ya ce kwamitin Nimi Briggs da aka ba makonni shida zai kammala aikinsa a ranar Juma’a. Daga nan ne gwamnatin tarayya za ta nemi ta yi zama da kowa.

Kara karanta wannan

Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden

Bayan nan, idan abin ya ci tura, Ministan kwadagon na kasa ya ce gwamnati za ta kai kara a kotu.

Vanguard ta rahoto Ministan yana cewa doka ta ce za a iya shigar da kara a kotun ma’aikata, idan har an gagara samun nasarar yin sulhu da kungiyoyin kwadago.

Yaushe za a koma aji?

Da aka nemi jin yaushe yajin-aikin zai kare, Ngige ya bada amsa da cewa zai tambayi kungiyar ASUU. Shi dai ya ce ana sauraron bukatun da malaman suka kawo.

A cewar Ngige, shi aikinsa kurum shi ne ya sasanta da ‘yan kwadago, amma Ministan ilmi da malaman jami’ar ne kurum za su san lokacin da za a koma karatu.

An yi watanni 2 ba a karatu

Tun a watan Fubrairu aka ji kungiyar ASUU ta shiga yajin-aiki a dalilin sabanin ta da gwamnatin Najeriya. Har yau bangarorin biyu ba su iya cin ma wata matsaya ba.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya caccaki Buhari, Shugabannin Najeriya yayin yi wa matasa kamfe

A watan Maris kungiyar malaman jami'an su ka yi zaman majalisar koli na NEC, su ka amince cewa a kara tsawon wa'adin yajin-aiki har sai gwamnati ta saurare su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel