Saraki: Idan na zama shugaban kasa, sai an nemi 'yan bindiga an rasa a Najeriya

Saraki: Idan na zama shugaban kasa, sai an nemi 'yan bindiga an rasa a Najeriya

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bulola Saraki ya lashi takobin kawo karshen ta'addanci da garkuwa da mutane idan ya zama shugaban kasa
  • Ya kara da alkawarin bai wa matasa da mata mukamai masu kauri a mulkinsa don kawo cigaba da hada kan mutanen kasa
  • Haka zalika, ya bayyana yadda shi da Bala Muhammad, gwamnan Bauchi suka nemi dattawan kasa don su sa musu hannu gami da basu shawararin masu amfani

Minna, Niger - Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa, ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa zai kawo karshen ta'addanci da garkuwa da mutane a kasar.

Yayin jawabi a ranar Lahadi a wani taro da wakilan zaben jam'iyyar PDP a Minna dake Niger, Saraki ya ce kasar na bukatar shugaban kasa mai jini a jika, The Cable ta ruwaito

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Kada Ka Ruɗa Ƴan Najeriya, Ƙungiya Ta Ja Kunnen Atiku

Saraki: Idan na zama shugaban kasa, sai an nemi 'yan bindiga an rasa a Najeriya
Saraki: Idan na zama shugaban kasa, sai an nemi 'yan bindiga an rasa a Najeriya. Hoto daga @bukolasaraki
Asali: Twitter

Wanda ke fatan darewa madafun ikon ya kara da cewa, idan aka zabe shi zai nada matasa da mata da dama a matsayin masu taimaka mishi wurin gudanar da milkinsa.

"Najeriya na bukatar shugaban kasa mai karsashi, jini a jika sannan kuma mai alkibila; shugaban da zai hada kawunan mutane gaba daya. Ni ne irin shugaban da Najeriya ke bukata. Idan na zama shugaban kasa, ta'addanci da garkuwa da mutane za su zama tarihi a wannan kasar. Ina tabbatar muku da cewa zan taka rawar gani a matsayin shugaban kasa," a cewarsa.
"Zan ba wa mata da dama mukamai a mulkina, kuma zan tabbatar na nada matasa a matsayin ministoci a kasar.
"[Shekarar]2023 ita ce lokacin da arewa ta tsakiya za su amshi mulkin kasa. Za mu kafa tarihi wajen samar da shugaban kasan da mutane suke so daga yankin. Za mu iya daidaitawa, cetowa, gami da sake gina kasar."

Kara karanta wannan

Ku yi koyi da Dangote: Buhari ya ba 'yan kasuwan Najeriya shawari mai ban mamaki

The Nation ta ruwaito cewa, tsohon shugaban majalisar dattawan ya kara da bayyana yadda yake goyon bayan turbar da ta samar da shi da Bala Muhammad, gwamnan Bauchi, a matsayin 'yan takarar da mutan arewa suka tsayar.

"Da kanmu muka je wurin dattawan kasa don neman goyon bayansu. Basu bukaci ko nemi su sa baki ba, kuma babu wanda ya tilastamu mu yi hakan," a cewarsa.
"Mun yaba da rawar da dattawan kasarmu suke takawa wajen kishi da burin hada kan kasa.
"Kiyaye abunda suka fada mana ya rage gare mu. Dole kowa yaje ya yanke shawararsa. Cikin saukin hali, na amince da abubuwan da suka bukaci mu yi, kuma mun fahimcesu, sannan na yanke shawarar dosar inda nasa gaba," ya kara da cewa.

A bangarensa, Babangida Aliyu, tsohon gwamnan jihar Neja, ya ce Saraki abun a dogara da shi ne.

"Akwai bukatar mu tsara matsayinmu, sannan mu bayyana bukatunmu. Saraki mutum ne da zamu iya dogara dashi," a cewar Aliyu.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Har yanzu ina shawarar takara, ku dakace ni: Goodluck Jonathan

2023: Ya kamata Atiku ya janye ya bar mun takara saboda kwarewata, Gwamna Muhammed

A wani labari na daban, Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya janye daga takara ya bar masa.

Gwamnan ya ce ya tara basira da damin kwarewa da zai iya jagorantar ƙasar nan idan ya zama shugaban ƙasa a 2023 ɗake tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng