Da duminsa: Har yanzu ina shawarar takara, ku dakace ni: Goodluck Jonathan

Da duminsa: Har yanzu ina shawarar takara, ku dakace ni: Goodluck Jonathan

  • Da alamun Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zai shiga takarar neman zama shugaban kasa
  • Jonathan ya fito ya yi jawabi da masu bukatar ya fito takara ranar Juma'a a birnin tarayya Abuja
  • Tsohon shugaban kasan ya ce su dakaceshi, har yanzu yana shawara kan tsayawa

Abuja - Bayan zanga-zanga da ihun sunansa da sassafe, tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, a ranar Juma'a ya fito don jawabi ga yan zanga-zangan da suka dira ofishinsa.

A jawabinsa, Jonathan ya bukaci matasan Najeriya sun zurfafa ra'ayinsu cikin siyasar Najeriya, rahoton Vanguard.

Tsohon shugaban kasan yace lokaci ya yi da ya kamata matasa su ci gajiyar dokar 'Not Too Young To Run Act'.

Yace yana sane cewa sun zo kira gareshi yayi takara amma ba zai ayyana niyyarsa yanzu ba saboda yana shawara.

Kara karanta wannan

'Dana mulkin da nayi lokacin da Buhari ke jinya yasa nike ganin na cancanci zama shugaban kasa: Osinbajo

A cewarsa:

"Na ji kuna kira gareni in fito takarar zabe, ba zan iya fada muku zan ayyana niyya ba. Ina shawara amma ku saurareni. Abinda ya zama wajibi kuyi shine Najeriya ta samu wanda zai dama da matasa cikin gwamnatinsa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Goodluck Jonathan
Har yanzu ina shawara takara, ku dakace ni: Goodluck Jonathan

Masoya Jonathan sun mamaye ofishinsa, suna neman gafara

Yayin da Najeriya ke kara kusanto da babban zaben 2023, a ranar Juma'a masu zanga-zangar sun mamaye ofishin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a Abuja, suna kira gare shi da ya ayyana tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Jama'ar sun kunshi maza da mata da matasa, inda suka mamaye ofishin dauke da alluna da takardu na neman tsohon shugaban kasar ya shiga takarar shugaban kasa

Wasu daga cikin fastocin da ke dauke da hotunan Jonathan an rubuta:

"GoodLuck Jonathan, dole ne ka tsaya takara"

Kara karanta wannan

2023: Shehu Sani ya hango yadda APC da PDP za su zabi 'yan takarar shugaban kasa

"Muna bukatar ka daidata Najeriya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel