2023: Ya kamata Atiku ya janye ya bar mun takara saboda kwarewata, Gwamna Muhammed

2023: Ya kamata Atiku ya janye ya bar mun takara saboda kwarewata, Gwamna Muhammed

  • Gwamnan Bauchi, Bala Muhammed, ya ce ya cancanci zama shugaban ƙasa ko dan kwarewa da basirar da Allah ya ba shi
  • Ɗan takarar ya yi kira ga Atiku Abubakar ya janye ya bar masa takara ƙarkashin PDP, saboda goyon bayan da yake da shi a faɗin ƙasa
  • A cewar Bala Muhammed, kowane ɗan takara na da ikon gwada sa'arsa, amma ya shirya tsaf ya karɓi mulki hannun Buhari

Bauchi - Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya janye daga takara ya bar masa.

Gwamnan ya ce ya tara basira da damin kwarewa da zai iya jagorantar ƙasar nan idan ya zama shugaban ƙasa a 2023 ɗake tafe.

Atiku Abubakar tare da gwamna Bala Muhammed.
2023: Ya kamata Atiku ya janye ya bar mun takara saboda kwarewata, Gwamna Muhammed Hoto: saheliantimes.com
Asali: UGC

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da yake tsokaci kan rikicin sulhu da nuna goyon baya dake wakana a jam'iyyar PDP yayin da ya bayyana a kafar Channels tv.

Kara karanta wannan

Jonathan na shirin komawa APC, sannan ya ayyana niyyar takara kujerar shugaban kasa

Tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja ya ce ya fi kowa shiryawa kasancewarsa matashi kuma mai jini a jika.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa gwamnan ya ce:

"Na shirya jan ragamar takarar kujera lamba ɗaya karkashin inuwar jam'iyyar PDP. Ina da karfi kuma gani matashi, na gina Gadoji kuma mutane na mun fatan alkairi a dukkan sassan ƙasar nan."
"Idan ka ga na yanje wa wani takarar shugaban ƙasa to yan Najeriya ne ko shugabannin jam'iyya suka juya mun baya."

Ko Jam'iyyar PDP ta shiga rudani ne?

Bala Muhammed ya ƙara da cewa idan aka bar lamarin takara tsakanin kudu da arewa, to abun ba zai haifarwa jam'iyyar PDP ɗa mai ido ba.

Ya ce yana da dumbin abokai a yankin kudu kuma yana da yaƙinin cewa idan tikitin takara ya faɗa hannunsa, waɗan nan abokan nasa zasu goya masa baya.

Kara karanta wannan

'Dana mulkin da nayi lokacin da Buhari ke jinya yasa nike ganin na cancanci zama shugaban kasa: Osinbajo

Gwamna ya ce goyon bayan da ya samu daga wurin dattawan arewa ba ya nufin zare sauran yan takara daga cikin tseren bane, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

A wani labarin kuma mun tattaro muku irin su Osinbajo, Tambuwal da sauran 'yan takarar shugaban kasa 10 da basu halarci taron Iftar din Aisha Buhari ba

A ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu, ne uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari , Hajiya Aisha ta gayyaci yan takarar shugaban kasa a fadin jam’iyyun siyasa zuwa taron buda baki.

Yayin da wasu yan takarar shugaban kasa daga jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) suka amsa gayyatar, wasu basu halarci liyafar cin abincin daren ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel