Sanatan APC Ya Bukaci Babban Hadimin Buhari Ya Bar Ofis Kan Sakaci 1 da ya yi

Sanatan APC Ya Bukaci Babban Hadimin Buhari Ya Bar Ofis Kan Sakaci 1 da ya yi

  • Sani Musa ya yi kira ga Babagana Monguno ya rubuta takardar murabus, ya sauka daga kujerarsa
  • Sanatan yace Janar Babagana Monguno mai ritaya ya gaza wajen aikinsa na bada shawara a kan tsaro
  • Nasir El-Rufai ya yi ikirarin Shugaba Muhammadu Buhari bai da labarin yana fuskantar barazana

Abuja - Sanata Sani Musa mai wakiltar Neja ta gabas a majalisar dattawa ya bukaci Janar Babagana Monguno mai ritaya ya sauka daga mukaminsa.

The Cable ta rahoto Sanata Sani Musa yana mai cewa akwai bukatar Hadimin shugaban kasar ya yi murabus saboda gazawarsa ta fito fili karara.

Kwanakin baya aka ji ‘yan ta’adda sun fito suna barazanar za su dauke Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da Mai girma Muhammadu Buhari.

Da aka yi hira da Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa shi ya fadawa shugaban kasar cewa rayuwarsa na cikin barazana, a lokacin sam bai da labari.

Kara karanta wannan

Sheikh Bello Yabo ya fusata, ya roki Allah yasa a sace Buhari, El-Rufai da Garba Shehu

Da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels TV, Sanatan yace tun da Hadimin ya gaza ankarar da shugaban kasa, bai dace ya cigaba da aiki ba.

Jigon na APC yake cewa hirar da aka yi da Gwamna El-Rufai ya nuna shugaba Buhari bai san halin da ake ciki ba, kuma hakan ya isa babban laifi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hadimin Buhari
Shugaban kasa da Babagana Monguno Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Idan gaskiya ne akwai matsala

“Idan har gaskiya ne abin da Gwamna El-Rufai ya fada cewa shugaban kasa bai san halin da ake ciki ba, wannan ya isa ayi waje da NSA.”
“Ana zubar da jini a kasa, amma wanda ya kamata ya tsara harkar tsaro bai san da maganar ba, kuma ba a sanar da shugaban kasa ba.”

- Sani Musa

Sanata Musa yake cewa rashin sanar da shugaban kasa game da barazanar da yake fuskanta babban laifi ne da ya isa mutum ya rasa kujerarsa.

Kara karanta wannan

Babbar matsala sabuwa ta kunno, Wasu Sanatocin APC sun goyi bayan tsige shugaba Buhari

Musa yace da shi ne a rigar Mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, da tuni ya rubuta takardar murabus saboda ya gaza tsare al’umma.

Sanatan na Neja yake cewa bai kamata hadimin ya jira sai an kai hari sannan zai dauki mataki ba, yace ya kamata a canza salo a yakin da ake yi.

Legas na cikin barazana

Kamar yadda kuka samu labari dazu, rundunar ‘Yan Sandan Najeriya tace ta san da yiwuwar miyagun ‘Yan ta’adda su aukawa mutanen Legas.

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Legas, Abiodun Alabi ya bayyana cewa a shirye dakarunsa suke, ya fadakar da al'umma da su bada hadin-kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel