Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

  • Wani dan takarar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya yayin da wasu 'yan bindiga suka farnake shi a Enugu
  • Wannan lamari ya tada hankalin jama'a, inda magoya bayansa suka bayyana alhini tare da yin Allah wadai
  • Ya zuwa yanzu, hukumar 'yan sandan jihar Enugu bata tabbatar da faruwar lamarin ba, amma shaidu gani da ido sun tabbatar

Jihar Enugu - Rahotanni sun bayyana cewa wani mai neman takarar majalisar dokokin jihar Enugu a zabe mai zuwa Mista Akaolisa Ogbe ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kashe shi da aka yi.

Wani ganau, Mista Okeke Aruma, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin, ya ce mahara sun harbi Ogbe ne a ranar Asabar, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sabon hari: ‘Yan bindiga sun budewa jama'a wuta, sun hallaka wani adadi mai yawa

Yadda 'yan bindiga suka so kashe dan takarar majalisar jiha
Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha da aka harba a gidan ya farfado | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Aruma ya bayyana harin a matsayin rashin hankali da rashin tausayi, wanda ke zuwa dab lokacin bikin Easter, lokacin da Kiristoci ke bikin tashin Yesu Kiristi mai tsarki, kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su kara kaimi wajen kare rayukan ‘yan Najeriya, yana mai gargadin cewa idan har haka ta ci gaba da faruwa zai tunzura 'yan Najeriya su ki fita zabe a 2023.

Wata kungiya mai suna Ogbe Akaolisa National Support Group, ta tabbatar da harin a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun wani Cif Christian Ezude.

Sanarwar ta kara da cewa, an tare da dan siyasar ne a cikin wani gidan mai tare da dirka masa harbin bindiga ta yadda zai iya mutuwa a ranar 16 ga watan Afrilun wannan shekarar.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun tsare mai tsohon ciki, ta na kokarin nakuda, su na neman kudin fansa

Hakazalika, kungiyar ta ce an yi yunkurin kashe shi ne jim kadan bayan kammala ziyarar neman shawarwari a unguwannin da yake neman tsayawa takara a yankunansu.

Sanarwar ta kuma ce:

“Jama'ar Enugu, wannan ne irin siyasar da muke so? Jama'ar Enugu, za mu kona komai a kan son ranmu ko neman mulki?”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, bai mayar da martani ga sakon tes da aka aike ta layinsa ba don jin ta bakinsa game da lamarin har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Ku kawo fansa ko mu kashe sauran: 'Yan bindiga sun hallaka mutum 3 da suka sace a Kaduna

A wani labarin, 'yan bindigar da suka yi garkuwa da wasu mutane a Anguwan Bulus da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna sun kashe uku daga cikin su sannan sun yi barazanar kashe wasu har sai an biya kudin fansa.

Kara karanta wannan

Farawa da iyawa: Takarar Shugaban kasar da Ngige zai yi a 2023 ta gamu da bakin jini

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa kakakin yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da kisan yana mai cewa:

“Na amsa kiran waya daga wasu mutane uku a safiyar nan cewa an tsinci gawarwakin mutum uku a kauyen Dutse a wani waje a cikin jeji. An kwashe gawarwakin zuwa asibitin Saint Gerald Hospital. Muna kokarin tattaunawa da kwamandan yankin domin tabbatar da ganin wadanda ke tsare sun dawo lafiya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel